✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

HOTUNA: Yadda mota ta fado daga saman gada a Abuja

Motar ta fado daga saman gadar da misalin karfe 3 na rana.

Hatsari ya rutsa wani mutum da abokinsa yayin da motarsu ta fado daga saman gadar shatale-shatalen Berger da ke Abuja.

Aminiya ta ruwaito lamarin ya faru a ranar Alhamis, yayin da motar kirar Toyota Camry ta fado daga kan gadar da misalin karfe 3:10 na rana.

Motar mai lamba ABJ 135 HF, ta fito ne daga yankin Area 1 ne, yayin da daya daga cikin tayoyin motar ta fashe, lamarin da ya kai kwace wa direban tare da fadowa daga saman gadar.

Wani ganau ya tabbatar da faruwar lamarin.

“Ina tare da abokina sai ga mota ta fado daga kan gadar, tare da taimakon sauran mutanen da ke kusa, mun samu nasarar kubutar da su tare da kai su asibiti.”

Ga hotunan motar: