✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan Arewa su yi taka-tsan-tsan a bikin binne Olubadan — Sarkin Hausawa

Ya nemi limamai da malamai su yi wa marigayi Olubadan na Ibadan addu’ar neman gafara.

Sarkin Hausawan Ojo Tudun-Sunnah a Ibadan, Alhaji Ali Yaro, ya yi kira ga dukkan ’yan Arewa a ko’ina suke a Masarautar Ibadan a Jihar Oyo su girmama bukukuwan al’adun gargajiya da aka saba yi duk lokacin da Olubadan ya rasu da bukukuwan nadin sabon sarki.

Ya ce, ya kamata ’yan Arewa musamman Hausawa su yi wa kansu kiyamulaili wajen janye jikinsu daga shiga cikin dodannin da suke zagaya cikin gari da sunan nuna alhini ga rasuwar Olubadan ko fitowa domin nuna murna ga sabon sarki.

Alhaji Ali Yaro ya yi wannan kira ne a sakon ta’aziyyar rasuwar Olubadan na Ibadan Oba Lekan Balogun.

Ya ja kunnen Hausawan da ke zaune a unguwannin birnin Ibadan cewa kada su kuskura su nuna kyamar su ga wadannan al’adu kuma kada su shiga ciki domin zama lafiya da kwanciyar hankali a Ibadan da Jihar Oyo baki daya.

“Ina ba mutanenmu masu sayar da kayan abinci da na bukatu a cikin garin Ibadan shawarar ku dakatar da harkokinku a tsawon yinin fitowar dodannin al’ada domin ana iya samun bara-gurbi da za su iya amfani da wannan dama wajen yin wasoson kayan da mutanenmu ke sayarwa su haifar da rikici,” in ji shi.

Ya nemi su kasance masu girmama doka da oda a kowane lokaci.

Sarkin Hausawan ya nemi limamai da malamai a masallatan Hausawa su yi amfani da wannan lokaci na azumin watan Ramadan wajen yi wa marigayi Olubadan na Ibadan addu’ar neman gafara.

Ya kuma bukaci su ci gaba da yin addu’o’in Allah Ya tsame kasar Najeriya daga cikin kuncin rayuwa da ya dabaibaye al’umma.