Ramadan: Babbar Tafiya!
Friday 28 July 2017     4 Zulki'da 1438

Aminiya

A+ A A-

Ramadan: Babbar Tafiya!

A Litinin da ta gabata ce al’ummar Musulmi muka tashi da ibadar Azumin watan Ramadan, xaya daga cikin shika-shikan Musulunci. Girma da muhimmancin da ke tattare da wannan ibada, dalili ke nan Bashir Malumfashi ya rubuta wannan gajeruwar waqa:

Alhamdu lillahi ni kam na xauki hanya
Na xau aniyar tafiyar isa birnin nahiya
Babban garin nan da babu kwaramniya
Garin da ba a shan ruwa na kwatanniya
Tafiyar nan fa ta faye nisa wane Zariya
Dole a doka sammako da jijjifin ita safiya
Na tanadi guzurin ruwa da tayoyi safaya
Ban buqatar abokiyar tafiya ko ita Safiyya
Aiki ne wurjanjan domin lahira nan duniya
Allah kare mu da kwazazzabo ko da zamiya
Burinmu mu isa zango mu sauka da lafiya
Musulunci gwadaben kirki wane qungiya
Shi ke jawo alherai tuli kullum iwa qugiya
Mun amsa mun bi mun aika ba wata tankiya
Allahu Al-afuwwu ga manzonKa ga sanayya
Ka sauqaqa mana tafarki mu sam ijara fiyayya
A wannan tafiyar Ramadan mun yo biyayya
Ka ba mu dace, mu sam kyakkyawar halayya
Mu zam tsarkin ruhi tsokarmu ta tsira, zuciya
Barka da zuwa ya Ramadana wata mai nuriya
Allah Ka kai mu garin nan mu cin masa lafiya

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited