Nazari: Mawaki Rarara da yankan kunkurun Bala (2)
Saturday 24 June 2017     29 Ramadan 1438

Aminiya

A+ A A-

Nazari: Mawaki Rarara da yankan kunkurun Bala (2)

Idan aka dubi irin wannan tsari a kasashen da suka ci gaba ta fuskar jari-hujja, za a ga cewa ita dukiya mallakar mai ita ce, gwamnati na sa baki ne kurum a cikin harkar gudanar da wannan dukiya wajen tabbatar da gudanuwar dukiya ta hanyar yin doka da inganta ko kyautata hanyoyin cin riba (da kuma riba) da samar da haraji ko kudin shiga.

Duk da cewa kasashe masu tasowa sun antaya cikin tsarin jari-hujja na duniya, sun yi haka ne ba tare da son su ba, wanda ya sa dole ake ganin birbishin tsarin mulki na gargajiya da kasashen suka gada can da tare da su. Da wannan tsarin danniya na gargajiya ne ’yan mulkin mallaka suka ci gaba da tatse da kuma tsotse arzikin al’umma masu tasowa duk da cewa sun shigar da nasu tsarin na zamananci.

Saboda haka shi wannan tsari na wariya da danniya ta hadin gwiwar sarakunan gargajiya da ’yan mulkin mallaka ya samar da rumbunan adabi. Ka-ce-na-ce da zage-zage da fadace-fadace da daure-daure da kuma kashe-kashe abubuwan nazari ne domin suna haifar da abubuwan nakaltar rayuwar al’umma, ya kuma samar da adabi ta hanyar baje kolin kungiyoyi da ra’ayoyi da suka dinga toroko a ruwa a lokacin fafutukar neman ’yancin Najeriya. Wannan zangon siyasa duk da cewa ba abin alfahari da murna ba ne ga wasu, ganin cewa zango ne da yawancin ’yan adawa ba su ji dadin rayuwa ba, amma wannan a maimakon ya sa jama’a su saduda, sai ma ya kara sa musu karsashi da ba su damar amfani da mabambantan dabashiri don yakar gwamnatin danniya da mulkin murdiya da kisan mummuke.
A duk lokacin da ake son a fahimci yanayin zage-zage da cin mutunci daga cikin ayyukan adabi, to ya dace a nakalci yadda danniya da babakera da kuma tashin-tashina ke wakana, ya kuma kamata a kalli matsalar ta fuskar su wane ne ake dannewa, su wa ke yin danniyar, kuma me ya sa ake yin danniyar, wace manufa ake son cimma wa? Ba za a ga amsar a fili ba sai an nakalci, an kuma yi nazarin dangantakar da ke tsakanin al’ummu da yadda ake gudanar da tattalin arzikin al’ummar bisa irin tsarin da ta ginu, musamman irin zaman kaskar da ke gudana tsakanin wadanda ake tatsa da irin tsarin da aka dasa domin tatsar tasu. Dangane da haka irin zaman doya da manja da ke tsakanin “tsarin tattalin arziki” da “tsarin mulki” a yawancin lokutta shi ke haifar da tsarin zaman dunniya da cin zali, ya kuma sa tsarin kaskanci ya ci gaba da tabbata.
Idan aka dubi irin wannan tsari a kasashen da suka ci gaba ta fuskar jari-hujja, za a ga cewa ita dukiya mallakar mai ita ce, gwamnati na sa baki ne kurum a cikin harkar gudanar da wannan dukiya wajen tabbatar da gudanuwar dukiya ta hanyar yin doka da inganta ko kyautata hanyoyin cin riba (da kuma riba) da samar da haraji ko kudin shiga. Duk da cewa kasashe masu tasowa sun antaya cikin tsarin jari-hujja na duniya, sun yi haka ne ba tare da son su ba, wanda ya sa dole ake ganin birbishin tsarin mulki na gargajiya da kasashen suka gada can da tare da su. Da wannan tsarin danniya na gargajiya ne ’yan mulkin mallaka suka ci gaba da tatse da kuma tsotse arzikin al’umma masu tasowa duk da cewa sun shigar da nasu tsarin na zamananci.
A Arewacin Najeriya, gargajiya ta saje ne da zamananci, masu mulki na gargajiya su ne suka daura aure da ’yan mulkin mallaka ta hanyoyi daban-daban, kuma ta haka suka amfana da juna. ’Yan mulkin mallaka sun tabbatar da samuwar tsarin mulkin En’e-En’e, suka yi wa tsarin shari’a kwaskwarima ya dace da tsarin mallaka, aka shigo da sababbin hanyoyin karbar haraji, Turawan mallaka suka baje kolinsu, suka ci karensa ba babbaka, kodayake a wadansu wurare karnukan sai da suka yi musu haushi, wasu ma da yakushi, duk da cewa an babbake su.
An kawo wannan dogon bayani ne domin mu fahimci cewa tashin-tashina da fafutukar samar da ’yancin kai a cikin kasa ba abu ne da kawai ake samu a gargajiyance ba, har da a zamanance. Tashin tashina ba wai ta tsaya ga amfani da karfin tuwo da ba hammata-iska a tsakanin mabambanta ra’ayoyi ba ne kurum, ko kuma tayar da kayar baya da ihuce-ihuce a fagen siyasa, musamman idan hakan ya tayar da hankalin wani ko wasu. Kodayake a nan ana maganar doka da tsari, sai dai ba mai iya cewa ga tashin-tashina da ke bisa doka ko kuma ga wadda ta saba ka’ida, ko kuma a ce ga inda ta ka’ida ta tsaya, ga inda wadda ba ta ka’ida ba ta soma.
A bisa wannan mataki za a gane cewa tashin-tashina ba ta tsaya ga mutum daya ba kurum, ta shafi kungiyoyi ko kuma gwamnati, ko baci da zagi ga ita gwamnati ko wani na kusa da ita, haka da yaki da abin da zai iya jawo yakin ko kuma rashin kwanciyar hankali da dai sauransu. Idan kuma aka dubi batun ta fuskar siyasa da kuma dimokuradiyya, za a ce ta shafi duk wata dama da aka hana wasu su yi amfani da ita wajen zama cikakkun ’yan kasa, musamman idan aka hana wasu yin amfani da damarsu ta zaben wanda suke so, ko a matsa musu su zabi wani can daban ko a hana su yin kamfen (yakin neman kuri’a), ko rashin daidaito wajen yin zabe, rashin ’yancin jefa kuri’a, yarda ko rashin yarda da sakamakon zabe, bisa amincewa da abin da jama’a suka zaba, uwa-uba hana maigida samun hanyoyin ciyar da iyalinsa ko a sa masa wasu matakai da za su hana shi ci gaba ta kowace irin hanya, yana tare da hukuma ne ko kuma dan adawa ne, balle kuma in hukuma ta kasa kare al’ummarta ko kuma ta kasa sama masu abubuwan more rayuwa.
A Arewacin Nijeriya, tashin-tashinar da za a buga misali da ita, mai kama da wannan da wakokin Rarara suka tayar ita ce wadda ta shafi matsi ga abokan adawa a jamhuriya ta farko, saboda sun yi wadansu abubuwa da hukuma ke ganin ba “daidai” ba ne, kamar sanya tutar jam’iyya a keke, sa bajen jam’iyya ko kuma kin da su wasu ke yi na zuwa gonar sarki domin noman gandu ko hakar kuza, ko noma hatsin kudi maimakon na ci, ta haka za a ga hoton rayuwar danniya karara da suka hada da kwace kayan ’yan adawa; gonaki ko dabbobi ko keken shanu ko kuma kwana da amaren ’yan adawa da dai sauransu. Ire-iren wadannan tashin-tashina da suka hada da kisan gillar ’yan adawa da hukumomin en’e-en’e suka asassa, tattare da taimakon ’yan doka da alkalai ta amfani da daurin gindin jam’iyyar NPC wadda ta mulki Arewacin Najeriya da kuma Gwamnatin Tarayya da ’yan mulkin mallaka ba sa misaltuwa. Wannan hatsaniya da ka-ce-na-ce da kuma tashin-tashina su suka haifar da siyasar Yankan Kunkurun Bala a tsakanin magoya bayan jam’iyyun NEPU da NPC, saboda zaman dirshan da jam’iyyar NPC ta yi na ganin wasu ’yan Arewa ba su shiga cikin harkokin mulki da gina kasa, tattare da ciyar da tattalin arzikin jama’a gaba ba.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited