Yadda harshen Hausa ya mamaye birnin Minna
Monday 26 June 2017     1 Shawwal 1438

Aminiya

A+ A A-

Yadda harshen Hausa ya mamaye birnin Minna

Duk wanda ya ji labarin birnin Minna da ke jihar Neja zai yi zaton gari ne da ake yin magana da harshen Nufanci ko harshen Gwari to amma da wakilinmu ya ziyarci birnin sai ya tarar harshen Hausa shi ne harshen da mutanen garin ke magana da shi a harkokinsu na yau da kullum.
Bincike ya nuna cewa birnin Minna gari ne da aka kafa shi tun shekarar 1910, wato kimanin shekaru 116 ke nan, amma bincike ya nuna cewa Hausawa suna birnin tun kimanin fiye da shekaru dari.
Aminiya ta gano cewa asalin birnin Minna gari ne wanda kabilar Gwari suka kafa, inda daga bisani sauran kabilu kamar Nufawa da Kadara da Koro da Hausawa da Yarabawa da Igbo da sauran kabilu suka zauna a garin.
Hujjojin da wakilin Aminiya ya tattara sun nuna cewa Hausawa kusan sun mamaye komai tun daga harkokin kasuwanci da mulki da kuma kananan sana’o’i. Sai dai kuma ilimi da kasuwanci su ne manyan abubuwan da Hausawan suka rike kuma su ne suka ba su damar suka yi fice kuma suka samu daukaka a kan sauran kabilun birnin.
Alhaji Abdullahi Aliyu Mu’azu shi ne mai rike da saurautar Fagacin Minna a fadar sarkin Minna na yanzu. Ya shaida wa Aminiya cewa Hausawa sun zo garin tun kimanin fiye da shekaru 100 da suka gabata. Ya bayyana cewa gaskiya da rikon amana ne ya sanya Hausawa suka yi fice kuma harshen Hausa ya samu daukaka fiye da kowane harshe a garin Minna.
“Hausawa sun dade a garin Minna. Gaskiya da rikon amana ne suka sa suka yi fice kuma harshen Hausa ya karbu kuma ya yadu cikin sauri.” Inji shi.
Ya bayyana cewa harshen Hausa shi ne yaren da mutanen jihar suke yin magana da shi tsakaninsu. Ya bayyana cewa Hausawa daga jihohi daban-daban kamar Sakkwato da Katsina da Kano da Jigawa da Bauchi da Zamfara da sauran jihohin Hausa sun shigo Jihar Neja ne sakamakon kasuwanci da malanta.
“Mafi yawan Hausawan da suka shigo, ’yan kasuwa ne da malamai. Sukan kawo kayayyaki daga kasar Hausa suna sayarwa sannan kuma malamai da yawa sun shigo da almajiransu don ci-rani da karatun Alkur’ani.” Inji shi.
Shi ma da yake karin bayani, Malam Usman Hassan, wanda ya yi fiye da shekaru 60 a birnin Minna; ya bayyana cewa kasuwanci shi ne ya yi sanadin zuwansa Minna. Ya bayyana cewa a birnin Minna ya yi aure ya haifi ’ya’ya da jikoki har ta kai wasu daga cikin jikokinsa ba su san garinsu ba saboda dadewar zamani.
“Ka ga ni kasuwanci ne ya yi sanadin zuwana. Huluna nake kawowa nan Minna, ina sayo su ne daga Kano da Borno. A nan na yi aure na haifi ’ya’yana da kuma jikokina har wasu daga cikinsu ba su san garinmu ba.” Inji shi
Shi Malam Sulaiman ya bayyana cewa hakuri da juriya su ne suka sanya Hausawa suka yi fice a Minna. “Ka san shi Bahaushe mutum ne mai karamci da yakana da kawaici, shi ya sa Gwarawa suka ji dadin zaman da shi suke girmama shi.” Inji shi.
Ya bayyana cewa tuni auratayya ta shiga tsakanin Hausawa da Gwarawa har ta kai wasu sun manta da asalinsu sun koma Hausawa sak.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited