Na ziyarci qasashen duniya 56, ina jin harsuna 18 - Marubuci Sharif Maidouki
Saturday 24 June 2017     29 Ramadan 1438

Aminiya

A+ A A-

Na ziyarci qasashen duniya 56, ina jin harsuna 18 - Marubuci Sharif Maidouki

Malam Sharif Maidouki fitaccen marubuci ne da ya zagaya duniya sannan qwararre ne a fannonin rayuwa masu yawa. Marubuci ne da ke jin harsuna da dama kuma ya iya rubutu da su.

Sananne ne a kafafen watsa labarai, musamman Freedom Radio Kano, inda yake gabatar da shirinsa da ke bayyana shige-da-ficen da ya yi a lunguna da saqunan duniya daban-daban. A kwanakin baya ne ya bayyana a shafin Duniyar Marubuta na Facebook, inda a shirin ‘Ga Wuri Ga Waina,’ membobin shafin suka yi ta yi masa tambayoyi daban-daban, shi kuwa yana amsawa. Mun kalato wasu daga cikin tambayoyin da ya amsa, kamar haka:

Ko za mu ji taqaitaccen tarihin Malam Sharif Maidouki?
A taqaice dai an haife ni a cikin birnin Kano, a Unguwar Warure, wadda a yanzu tana cikin Qaramar Hukumar Gwale. A yanzu dai shekaruna 51 daidai a duniya. Na fara karatuna na Alqur’ani a wajen mahaifiyata, sannan na dawo zauren gidanmu na ci gaba da karatun tare da da ’yan uwana, a wajen malaminmu mai sunan Malam Nasir. Daga baya aka mayar da ni makarantar Alqur’ani ta Sharu Amadu (Allah Ya jiqansa da gafara), wadda take Lungun Darma, tun kafin a fito da ita bakin titin Kwanar Gabari.
Kana na yi karatu a Ma’ahhad Deen Islam ta Sheikh Nasiru Kabara, wadda take Unguwar Gwale. Daga nan mahaifina ya kai ni qasar Saudiya domin na ci gaba da karatun a can, ina kamar xan shekara 8 zuwa 9. A qasar ta Saudi na gama karatun Iftida’iyya da Sanawiyyah, kana kuma na shiga babbar makaranta. Wasu dalilai suka sanya na dawo Najeriya. Bayan wata uku da wannan ne na shiga uwa duniya.
Bayan shekara biyar da shigata duniya ne na koma qasar Saudiya, na qarasa Diplomata a kan fannin karatun da na fara na Shari’a. Daga baya kuma na yi tunanin canja fannin karatun nawa gaba xaya, ganin Allah Ya yi ikon ni ba mazaunin qasata ba ne. Don haka na je qasar Netherlands (Holland), na karanta fannin Gona, abin da ya shafi kayan marmari da ’ya’yan lambu.
Bayn wasu shekaru kuma na koma qasar Indiya (wadda daman kamar qasata ce). Na yi karatun fannin lafiya, alhamdu lillahi na fara shi da girmana sosai, kuma na fara ne daga Clinical Assistance har sai da na kai matsayin da likita zai yi karatu a fannin wani vangare na jikin bil Adama. Batun iyali kuwa, ina auren mata biyu kuma ina da ’ya’ya 12, guda shida mata, shida maza. Wannan shi ne a taiqace, tarihina.
Kana jin yare da yawa, wane qalubale ka fuskanta wajen koyon yarukan kuma waxanne ne ka iya rubutu da su kuma wane yare ka fi qauna daga cikinsu?
Ina jin yaruka 18, kuma na fi son yin rubutu a cikin harsunan Arabi, domin yaren gidanmu ne. Sai kuma ina jin daxin rubutu da yaren Indonesiya da kuma Swahili da kuma French.
Sirrin koyon yarukan kawai shi ne, Allah Ya ba ni dama na yi yawon duniya, tun daga Kano har ya zuwa Nagasaki ta qasar Japan, sannan na gangaro na dawo Mumbai ta qasar Indiya. Duk wannan yawo da na yi, na yi shi ne a mota da jirgin ruwa, sannan kuma a matsayin lebura. Duk qasashen da na zauna kuma na koyi yarensu, domin na zauna ne a cikin talakawa kuma a unguwanninsu, inda kusan ba su da wani yaren sai nasu kawai. Wannan shi ne ya sa na koyi yarurrukan da nake ji, in ban da Arabiyya, domin shi Larabci daman yaren gidanmu ne.
Kamar yadda n ace, ina jin yaruka goma sha takwas, kamar haka: 1-Larabci, 2-Hindi, 3-Swahili, 4-Somali, 5- Amharic, 6-English, 7-French, 8-Turkish, 9-Spanish, 10-Italiano, 11-Malay, 12-Indonesia, 13-Fashtoush, 14-Djzarma, 15-Tamashak, 16-Yoruba, 17-Igbo, da kuma 18-Hausa.
Batun rubuce-rubuce fa, littafi nawa ka rubuta?
Na rubuta littattafai har guda 21, waxanda suka haxa da ‘Shiga Duniyar Sharif Medouki’ na 1, ya shiga kasuwa tuni. Sai kuma littattafan tarihin Arewacin Najeriya, waxanda na ba su sunan ‘Lardunan Arewa Da Qabilunsu’ na 1 zuwa na 19. Kowanne littafi na ba shi laqani da sunan Lardi ko Jiha a yanzu. Misali, littafin Lardunan Arewa Da Qabilunsu Daular Hamma Ruwa, tun ranar miqa wa Sarkin Muri Jidda Tafida sanda ya shiga kasuwa. Sauran ma in sha Allah suna tafe. Sai kuma littafin ‘Shiga Duniyar Sharif Medouki (Cikakken Labari)’ zai fito in sha Allah nan da Sallah babba.
Me za ka iya cewa game da tasirin marubuta cikin al’umma? Wacce shawara za ka ba matasan marubuta masu tasowa?
Murubuta suna da tasiri matuqa a cikin kowace al’umma a duniya. Abin takaici, a nan qasar Hausa shi ne, su da kansu murubutan ba duka ne suka san darajar da Allah Ya yi musu ba, har ya zama wasunsu suna vata basirar da Allah Ya ba su ta inda bai dace ba.
Game da shawara kuwa, ina kira ga marubuta da su riqa yin biyayya ga manyan murubutan kuma su riqa koyon qa’idojin Rrubutu, su riqa yin rubutun a fannoni daban-daban.
Yaya za ka kwatanta rubutun jiya da na yau? Ci gaba aka samu ko baya? Shin ko yawaitar marubuta da kuma samuwar littattafai rututu a yanzu fiye da shekarun baya ya taka rawar cig aba ko kuma baya?
Gaskiya a wannan kusan sai na ce ba a samu wani ci gaban a zo a gani ba. Dangane da cewa in aka kwatanta rubutun dauri da na yanzu kuwa, yawaitar rubutu bisa jigo xaya, ko yawan kwaikwayon rubutun murubutan yanzu, ko kuma taqaita rubutu bisa mas’ala xaya, shi ya sa nake ganin ya kamata murubuta su sake salo.
Batun littafina day a fita kasuwa kuwa, ina da masaniyar cewa a yanzu babu shi a kasuwa, ya qare da jimawa. Amma in sha Allah, nan da Sallah babba za a samu cikakken littafin a kasuwanni da shaguna. Ina maganar littafin ‘Shiga Duniyar Sharif Maidouki’ ne, littafin da ni kaina na san akwai faxarkarwa da ilmantarwa, tausayawa da kuma abubuwan ban dariya, har ma da na ban haushi.
Kasancewarka gogagge, wanda ya yi yawo a duniya, yaya kake ganin yanayin al’adun waxancan mutane da mu nan na Hausawa, namu ya fi nasu ko nasu ya fi namu?
Gasiya akwai bambance-bambance sosai tsakanin al’adun qabilun duniya, domin abin da ke daidai a wata qabilar, kuskure ne wata ne. Misali, a zamana a qasar Somaliya, na kula zai yi wuya a wancan lokacin ka ga saurayi da budurwa sun yi aure da yardar iyayensu a qasar. Sannan a qasar Indiya, mace ce za ta ba namiji sadaki. A qasar Isra’ila, za ka yi mamaki yadda matsayin ’ya’ya suke a wajen iyayensu. Haka kuma a qasar Thailand, abin mamakin da za ka sha shi ne yadda aka xaure wa fasiqanci gindi, kuma ba laifi ba ne. Domin a qasar ce na fara ganin inda ake ba mazinaci rasixi (receipt) tun kafin ya aikata masha’ar. Akwai dai wasu abubuwan mamaki masu yawan gaske. Qasashen Indiya da kuma Ethiopia (Habasha) sun fi yi mini kama da al’adun Hausa/Fulani qwarai da gaske.
A yawace-yawacena, qasashe 56 da na je a duniya, na fi jin daxin zaman qasar Indiya, domin har zancen yanzu da nake nan Najeriya tare da ku, kashi 85% na samuna daga hanyar Indiya yake zuwa cikin ikon Allah.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited