Ina matukar farin ciki da kasancewata marubuciya - Fatima Danbarno
Friday 28 July 2017     4 Zulki'da 1438

Aminiya

A+ A A-

Ina matukar farin ciki da kasancewata marubuciya - Fatima Danbarno

Fatima Ibrahim Danbarno ta kasance matashiyar marubuciyar littattafan Hausa. A tattaunawarta da Aminiya, ta bayyana al’amura   da dama dangane da harkar  rubutu da marubuta da kuma dangantakarsu da al’umma:

A takaice, ko za ki bayyana mana tarihinki?
Kamar yadda ka sani, sunana Fatima Ibrahim Garba (danborno). Ni haifaffiyar garin Zariya ce, Jihar Kaduna. An haife ni a ranar 12 ga Oktoba, 1993 kuma iyayena ’yan asalin garin Borno ne, a karamar Hukumar Kwaya. Na yi makarantar firamare ta Fala’ul Umma da ke birnin Zariya. Ban kai ga karasawa ba, na koma Abubkar Maccido. Na yi karatun sakandare a G. S. S. kofan Kuyanbana, Zariya. A yanzu haka ina karatu a F. C. E Zariya, ina nazartar Hausa/English.
Kin kasance marubuciya, tun yaushe kika fara harkar rubutu kuma me ya jawo hankalinki ga haka?
Eh to, na fara rubutu tun a 2007. Abin da ya jawo hankalina ba zai wuce sha’awar abun ba da kuma bayar da gudunmawata, kasancewar a lokacin ina karance-karance wanda na karu da abubuwa masu yawa. Marubuci yana da wata baiwa wanda ba kowa ya san da wannan baiwar ba. Ganin ina karuwa ya sanya ni ma na ji zan iya taimakawa har jama’a su amfana da kalar tawa fadakarwar.
Wane littafi kika fara rubutawa kuma ya shiga kasuwa, kuma mene ne jigonsa?
Na fara rubuta littafin ‘Zuciya’ amma ba shi na fara fitarwa ba, littafin ‘Kowa Ya Kwana Lafiya’ ne ya riga fita kasuwa. Jigon littafin kuwa shi ne, nasiha ce da jan hankali cikin ruwan sanyi, a kan yadda yawancinmu mata muke da girman kai, ba mu girmama duk wanda ke gabanmu. Babban burin wasunmu ba zai wuce mu ga muna juya duk namijin da ya dube mu ya ji yana sonmu ba. Da haka ne na dauki wannan jigon na kuma nuna cewa da mulki da kudi da ilimi, duk Allah ke ba da wa, a lokacin da Ya so, Ya kuma canza maka rayuwa a lokacin da Ya so. Ma sha Allah! Sakon da na yi kokari don ya isa ya kai inda nake bukata.
A wace shekara littafin ‘Kowa Ya Kwana Lafiya’ ya fita kuma kwafi nawa kika sayar?
A shekarar 2012 ya fita kasuwa kuma kwafi dubu daya aka buga, kuma na sayar da su.
Ya zuwa yanzu, littattafai nawa kika rubuta kuma guda nawa suka shiga kasuwa?
Na rubuta littattafai za su iya kai takwas. Hudu sun fita, uku sun shiga kasuwa, sai kuma daya da nake sa ran nan da wata daya zai iya fitowa. Wadanda suka fito su ne: ‘Kowa Ya Kwana Lafiya’ da ‘Zuciya’ da ‘Sirri’ sai kuma ‘Ina Muka Dosa?’ Wanda zan saki nan da wata daya, shi ne ‘Mafarin Lamarin.’
Yaya batun littafin da kike shirin kaddamarwa a watan gobe? Yaya sunansa, mene ne jigonsa?
Batun kaddamar littafi yana nan in sha Allahu. Littafin da zan kaddamar ranar 6-08-2016 in sha Allah, sunansa ‘Ina Muka Dosa? Ya zuwa yanzu an kammala aikin buga shi, jira muke kawai lokacin kaddamar da shi ya yi. Jigo biyu na yi amfani da su a cikin littafin. Jigo na farko a kan yadda iyaye suke tura ’ya’yansu almajiranci ne, ba tare da wata kulawa ba. Hasalima sukan mance girman amanar da Allah Ya ba su. Na biyu kuma a kan illar da ke tattare da dora wa yara mata talla suna fita titi ne, yadda abubuwa da dama suke faruwa da su a kan wannan tallar, wanda duk yana cikin kauce wa rikon amana.
Cikin littattafan nan naki, wanne ya fi kwanta maki a rai, kika fi ji da shi kuma saboda me?
Na fi son littafin ‘Sirri’ saboda shi ya fito da ni har duniya ta san ni. A batun littafin da na fi ji da shi kuwa ba zai wuce ‘Ina Muka Dosa’ ba. Dalilina kuwa shi ne, ya tabo min abin da na dade ina son rubutawa, musamman saboda iyayenmu. Ina son nuna wa iyaye da wadanda suke shirin zama iyaye illar da ke tattare da banzatar da ’ya’ya da kuma yadda suke kokarin fifita boko a kan karatunmu na allo da na Islamiyya.
Idan kika kalli kanki a matsayin marubuciya, yaya kike ji a ranki, kina jin gamsuwa ko kina yin nadama?
Eh, gaskiya da farko na yi nadamar kasancewata marubuciya, musamman da na fara samun rashin uzuri a wurin makarant na da kuma kawayena da muka jima tare. Ina jin daci a raina idan akayi min gurguwar fahimta, har a kira ni da mai girman kai. Kamar lokacin da nake rubuta littafin ‘Sirri’ na rika samun sako na bakar magana daga kawayena, cewa yanzu ina da girman kai, wanda su ba su sani ba ne, ban taba rubuta littafin da na sha bakar wuya ba, kamar ‘Sirri.’ Shi ya sa na ware kaina don in san me zan rubuta, ba tare da na kuskuro ba. Yanzu kam alhamdu lillahi! Idan ina kallon kaina a matsayin marubuciya nakan tsinci kaina a cikin nishadi, musamman ma da na hadu da masu kaunar aikina, suna kara mini kwarin gwiwa.
Me ke burinki na gama game da harkar rubutu, ko kina da shirin maida wasu littattafanki zuwa fim, ganin yadda sauyi ke faruwa a harkar?
Eh..... gaskiya ina sha’awar mayar da littafina ‘Sirri’ zuwa fim, wanda a yanzu haka ma na tsara labarinsa da kaina, na mika shi a gun jarumin nan, Adamu Zango. Amma in sha Allahu ina tunanin in dai rubutuna ne aka yi fim da shi, akwai fadakarwa da kuma nuna illar aikata wasu abubuwa da ba masu kyau ba ne. Sannan ina iya bakin kokarina wajan kamanta kawo tasirin addini a cikin labaraina, musamman ma da na yi kokari wajan kawo tasirin karatun Alkur’ani da sanya hijab da kuma yadda ’ya’ya mata a jami’a za su kare mutuncinsu daga sharrin aikata sabo. Sannan na yi kokari matuka wajan nuna ganganci a kan yadda mace za ta watsar da girma da mutuncin da Allah Ya ba ta.
Burina a harkar rubutu kuwa ba zai wuce in ga manyanmu sun san da zamanmu ba, sun karbe mu a matsayin masu muhimmanci. Mu ma za mu ji dadi, musamman ma idan suka kalli gudunmawar da muke bayarwa, duk da a yanzu na ga an fara sanin mahimmancinmu. To, a gaskiya burina ke nan. Ina rokon Allah Ya sa kafin in bar rubutu in ga ranar da za a san amfaninmu a wannan harkar.
Daga karshe, ko kina da shawara ko kira ga marubuta da gwamnati da kuma al’umma masu karanta littattafanku?
Shawarata za ta fi karkata ne ga gwamnatinmu saboda a littafina na ‘Ina Muka Dosa?’ kusan na karkata ne da halin da muke a yanzu, na yadda Gwamnanmu yake iya bakin kokarinsa na ganin an daina tallace-tallace da sauransu, wanda ni a ganina wannan laifi ya fi yawa ga iyaye. Wane mutum ne zai haifi dansa, ya kai shi almajiranci babu kudin omo bare na sabulu; ya mance da shi ma kwata-kwata?  A ganina, idan har aka tilasta wa iyaye ziyartar ’ya’yansu duk karshen wata don su dinga tattaunawa suna jin matsalarsu, suna kuma nuna masu mahimmancin wannan karatu na addini, to da matsala ba ta yi yawa a kasar nan ba. Ina jin haushin yadda idan makarantar kwana ce, za ka ga malamai suna matsa wa iyaye a kan zuwa kawo ziyara. Daga nan ne iyaye suke gane damuwar da ’ya’yansu suke ciki. Duk da na san wannan aiki ne mai wuya, amma idan aka dage in sha Allahu za a samo wa yara masu tasowa ’yancinsu.
Marubutanmu har gobe ba zan daina ba ku shawarar ku dinke ku zama tsintsiya daya ba. Duk da alhamdu lillahi,  na ga yanzu komai yana tafiya lafiya. Zan sake yin amfani da wannan dama wajan kara rokon masu karanta littattafanmu a kan su kara hakuri da mu, su ci gaba da yi mana uzuri.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited