Yadda za a inganta harkar rubutu a Najeriya – Larabi
Saturday 24 June 2017     29 Ramadan 1438

Aminiya

A+ A A-

Yadda za a inganta harkar rubutu a Najeriya – Larabi

Abdullahi Jibril dankantoma wanda aka fi sani da Larabi, fitaccen marubuci ne da ya dade a harkar rubutu. Ya rubuta littattafai fiye da 10, a cikin hirarsa da Aminiya ya bayyana abin da ya ja hankalinsa ya shiga harkar rubutu, matsalolin da suka hana shi fitar da littafi da kuma hanyar da za a bi wajen inganta rubutu a Najeriya. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

Aminiya: Za mu fara da tarihinka a takaice
Larabi: Sunana Abdullahi Jibril dankantoma. An haife ni a birnin Kano a 1979. Na yi karatun addini har na sauke Al’kur’ani maigirma, sannan na yi karatun wasu littattafan addini. Na yi karatun boko har na mallaki HND a kwas din Banking and Finance a Kano State Polytechnic. Sannan na mallaki shaidar NIM (Chartered). Ga bangaren iyali kuwa a watan Fabrairu, 2016 na yi aure.
Aminiya: Ko za ka fada mana dalilin da ya sa ake kiranka da Larabi bayan sunanka Abdullahi?
Larabi: To shi ma Larabi din sunana ne na gida. A gida ake kirana da Balarabe. Ko Bala. Daga baya na yi wa sunan kwaskwarima na cire ‘Ba’ na farko ka ga saura ‘Larabe’, to shi ne nake amfani da shi kuma tun kafin na fara rubutu nake amfani da shi ba wai sai da na fara ba ne.
Aminiya: Me ya ja hankalinka ka shiga harkar rubutu?
Larabi: Abin da ya ja hankalina na shiga harkar rubutu shi ne, yawan karance-karance da kuma son ni ma in bada tawa gudunmawar wajen fadakar da al’umma kan wasu matsalolin da ya kamata su gyara.
Aminiya: Zuwa yanzu littattafai nawa ka rubuta, wanne ka fi so, kuma me ya sa?
Larabi: Zuwa yanzu na rubuta littattafai 11, wadanda suka hada da ‘Buwaya’ da ‘Komai Dadinki Da Miji’ da ‘Gudun kaddara’ da ‘Sirrin So’ da ‘Sakaci’ da ‘Maza Tabarmar kashi’ da ‘Wata Sabuwa’ da ‘An Yi Ba A Yi Ba’ da ‘Karan Tsaye!’ da ‘Kuskure Na Yi’ da kuma ‘Kaza Da Hanjin Sarka’. Duk ina son su, amma in ya zama dole sai na zaba zan iya zabar ‘Gudun kaddara’ da ‘Komai dadinki Da Miji’
Aminiya: Me ya sa?
Larabi: Saboda littafin ‘Komai Dadinki Da Miji’ ne ya daukaka darajar sunana a duniyar rubutu. Shi kuma ‘Gudun kaddara’, ingancin labarinsa ya yi nisan da mutane da dama sun amfana da shi, har yau ana amfana da labarin, kuma ana yaba mini kan namijin kokarin da na yi wajen fadakar da mutane kan abin da ya shafi zamantakewar aure da kuma sauran rayuwar da ta shafi addini.
Aminiya: Wasu suna tunanin kana amfani da sunan Larabi ne saboda lokacin da ka fara rubutu mata ne ke juya akalar kasuwar littattafan Hausa, hakan ya sa ka yi amfani da sunan, kasancewar yana kama da sunan mata don ka batar da hankalin makaranta su dauka cewar kai ma mace ne, me za ka ce game da hakan?
Larabi: Ka san ita fahimta fuska ce. Kuma ba zan hana mutane fadar ra’ayinsu ba. Amma a zahiri ba haka ba ne. Don wasu marubutan sun yi zaton hakan, sai suka canja sunayensu kuma suka ga sabanin hakan, domin kasuwa ta yi alkalanci. Shi suna ba ya sayar da littafi. Dadin labari da ma’anarsa ke sayar da littafi. Ina jin in har ban yi kuskure ba ai akwai mata da yawa da na fi su karbuwa a wancan lokacin din. Ka ga da a ce haka hasashen yake tun da su mata ne da ban isa in sha gabansu ba.
Aminiya: Salon rubutunka ya yi kama da irin na mata ko me ya sa kake yin hakan maimakon ka yi irin salon rubutun maza?
Larabi: A rubutun Adabi babu wani salo da aka ware aka ce wannan shi namiji zai yi amfani da shi. Haka ba a ware wa mata salonsu ba. Abin da ya zo daga baya dai kawai su mata sun zabi su yi rubutu a kan matsalolin da suka shafe su ne don sharewa ’yan uwansu mata masu irin wadannan matsalolin hawaye. To kuma hakan ita ce matsalar da ta yi tasiri a rayuwarmu ta Hausawa. Ma’ana, matsalolin mata na gidajen aurensu da rayuwarsu gaba daya tun daga tashinsu har zuwa girmansu, sun fi yawan matsaloli tare da rashin sanin yadda za su warware su fiye da maza. Don haka tun da ina da gudunmawar da zan bayar a kan matan sai na dauki bangarorin mata.
 Aminiya: A yanzu ba a ganin littattafanka, me ya sa?
Larabi: Abin da ya sa ba a ganin littafina shi ne, na kwana biyu ban yi rubutu ba. Ina jin rabon da na fitar da sabon littafi tun 2011, saboda harkokin kasuwanci da suka sha kaina, inda nake tafiye-tafiye ina saro kaya da kuma rabawa. To mawuyacin abu ne harkokin su hadu da rubutu. Amma dai har yanzu rubutu yana raina kuma ina da burin sake dawowa harkar, don ci gaba da bada gudunmawata ta fuskar addini da kuma zamantakewar aure.
Aminiya: Marubuta da yawa sun koma rubuta labarin fim, me hana ka canza sheka kai ma?
Larabi: Gaskiyar magana lokacin rubutun ne ya yi mini karanci. Amma ina da sha’awar hakan. Kuma wasu daga cikin furodusoshin da suka san rubuce-rubucena ko kuma aka ba su labarin rubutun nawa sun nemi mu yi tafiyar tare, amma sai na ba su uzurina. Kadan daga cikinsu akwai irinsu Chali da Aminu Maje da kuma Nura Manager. Kuma su ma kansu marubuta abokaina da suke harkar sun yi kokarin jawo ni, amma lokacin yin rubutun yanzu shi ne matsala. Marubuta irinsu Nazir Adam Salihi da Maje el-Hajeej da Ibrahim Birniwa da Dauda Shafi’u Giwa da sauransu sun so in shiga harkar a dama da ni, amma lokaci bai bar ni ba.
Aminiya: A ganinka mece ce babbar matsalar harkar rubutu, wacce hanya za a bi wajen kawo gyara a harkar rubutu?
Larabi: Matsalolin harkar rubutu suna da yawa. Ka ga akwai matsalar kasuwanci. Ba ma fadada harkar kasuwancinmu. Tun da aka fara rubutun har zuwa yanzu hanya dai daya ce ake bi. Ba a zamanantar da ita bare kuma a ingantata. Sai matsalar rashin wadataccen kudi a hannun marubuta, wannan yana ba su gibi sosai wajen rashin inganta ayyukansu tare kuma da fadada harkokin kasuwancinsu. Akwai kuma rashin ingancin labarin da kuma yin salon da zai ja hankalin makaranta, shi ma gibi ne babba da yake bada  matsala a harkar rubutu.
Hanyoyin da za a bi a gyara kuwa su ne, marubuta su daure su dinga inganta ayyukansu tare da samar da labarai masu dadi da inganci, wadanda za su fadakar da al’umma, sannan su daure wajen fadada harkokin kasuwancinsu a zamanance.
Aminiya: Marubuta maza da yawa sun sare, inda aka bar mata wajen juya akalar rubutu, a ganinka me ya jawo hakan?
Larabi: Ba wai maza marubuta sun sare sun bar mata suna juya harkar ba ne. Matan ne suka yi wa harkar rubutu yawa, sannan gaskiyar magana sun fi maza kokarin kawo labaran da kasuwar rubutun take so fiye da mazan. Har yanzu akwai takwarorinmu maza da ke yin rubutu sai dai sun yi karanci ne.
Aminiya: An kafa kungiyoyin marubuta irinsu ANA da HAF da sauransu, kana ga wadannan kungiyoyi na taimaka wa marubuta?
Larabi: Eh to kai tsaye ba zan ce ba sa taimaka wa marubuta ba. Amma dai a hakikanin gaskiya tallafin da suke ba marubuta tun daga farkon fara rubutun su zuwa fitar da shi da kuma kasuwancinsa har yanzu ba wani na a zo a gani ba ne. Ya kamata su rika tsoma kansu wajen gudanar da harkar kasuwancin littafi.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited