Rubutun labarin fim yana bukatar lokaci- Fauziyya D. Sulaiman
Monday 26 June 2017     1 Shawwal 1438

Aminiya

A+ A A-

Rubutun labarin fim yana bukatar lokaci- Fauziyya D. Sulaiman

Fauziyya D. Sulaiman marubuciyar litattafan Hausa ce, ita ce Jami’ar Hulda da Jama’a ta kungiyar Marubuta ta Mace Mutum. Baya ga rubuce-rubucen litattafan Hausa tana rubuta labarin finafinan Hausa.

A yanzu haka Fauziyya ma’aikaciyar gidan talabijin na Arewa 24 ce, a tattaunawarta da Aminiya, ta yi karin haske game da matsalar da marubuta labarin fina-finan Hausa ke fuskanta wajen rubutu da sauran batutuwa:

Aminiya: Za mu so jin tarihin rayuwarki a takaice?
Fauziyya: An haife ni a unguwar Fagge a Kano a shekarar 1981. Na yi karatun firamarena a Makarantar Festibal da ke Kano. Bayan na kammala sai na tafi makarantar ‘yan mata ta  GGSS ‘Yargaya. Da na kammala karamar sakandire sai na tafi makarantar sakandiren GGC Dala inda na kammala a shekarar 1988. Bayan na kammala da shekara daya sai na yi aure. Bayan na yi haihuwata ta biyu sai na koma makaranta, inda na yi diploma a bangaren Food and Nutrition and Dietician a Makarantar Hygiene da ke Kano. Bayan haka na samu wata diplomar a bangaren girke-girke a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kano. Daga nan na samu shaidar wata diplomar a bangaren na’ura mai kwakwalwa. A yanzu haka ina da aure da kuma yara shida. Baya ga harkar rubuce-rubuce da nake yi ina kuma aiki da gidan talabijin na Arewa 24.
Aminiya: Ya aka yi kika fara rubuce-rubuce?
Fauziyya: Ba zan iya cewa ga yadda aka yi na fara rubuce-rubuce ba. Zan iya tunawa tun ina firamare nake da sha’awar karance-karance, wanda hakan shi ya ba ni dama har na fara rubuce-rubuce. A lokacin nakan rubuta litattafai na ajiye. Wasu lokutan nakan karantawa kawayena da yan uwana, su yi ta dariya. A haka na rika yi har na je sakandire na ci gaba da rubuce-rubucena. Da na yi aure ban fasa rubutun ba sai ma abin da ya yi gaba. Anan kuma sai Allah ya sa muka yi makwabtaka da wani marubuci mai suna Kabiru Anka. Nakan karbi litattafai a wurinsana karanta a rana sai na karanta litattafai. har wata rana nake gaya masa cewa ni ma fa ina da litattafai da na rubuta. Sai ya nemi na kai masa su, daya karanta sai ya ba ni karfin gwiwar yin rubutu har yana fadin ai tuni ma ni marubuciya ce ban sani ba. Anan na karkade tsofaffin rubuce-rubucena na gyara wanda zan gyra na kai a buga min a shekrar 2002. daga nan harkar rubutu ta bude min.
Aminiya: Zuwa yanzu liattatafai nawa kika rubuta?
Fauziyya: Na rubuta litattafai a kalla guda 30. Daga cikinsu akwai littafina na farko Me na yi mata? Burin raina da Rayuwar ‘Ya mace da Mece ce rayuwa da Guduna yake da Da me ake ado da kishin banza da karshen wahala da  Labarin Fauziyya da sauransu.
Aminiya: Ya aka yi kika canza kalar rubutunki zuwa rubutun labarin fina-finai?
Fauziyya:Har yanzu ban daina rubuta littafi ba, sai dai kawai na kara da rubuta labarin fina-finai. Kin san abin da ya ja hankalina ga rubuta labarin fina-finai shi ne akwai wani marubucin labarin fim wanda shi ma tsohon marubuci ne, Ibrahim Birniwa. Shi ya kwadaita mana rubutun fina-finai.  To tun daga nan sai na ji ina sha’awar rubutun fina-finai anan na nemi ya nuna min yadda ake yin rubutun. Tun daga wanann lokacin sai na shiga inda na fara da daukar litatatafaina guda biyu na mayar da su labarin fim. Sai na dauki labarin guda daya na ba wa wani Darakta Yasin Auwal sai ya yi fim din Uwargida da shi. Ganin cewa labarin ya samu amsuwa a wuirn jama’a ya sa daraktocin fim suka rika kirana suna ba ni aikinsu. To tun daga wanann lokaci na shiga harkar rubuce-rubucen finafinai gadan-gadan har zuwa yanzu. A wasu lokutan daraktocin kan sayi littafi kai tsaye daga hannun marubuci su je su tsara shi yadda zai zama labarin fim. Yayin da wasu lokutan kuma sukan neme ka kai marubuci su nuna suna so ka mayar da wani littafinka zuwa labarin fim. Anan za ku yi ciniki su biya ka kudinka.
Aminiya: . Mene ne bambanci tsakanin rubutun littafi da na fina-finai?
Fauziyya: zan iya cewa banbanci kalilan ne. Abin da ya bambanta su shi ne hanyar da ake bi wajen rubutun. Shi littafi rubutu ne na zube. Yayin da shi kuma rubutun finafinai ana rubuta shi ne bisa tsarin wasan kwaikwayo. Har ila yau wani bambancin da ke tsakanin rubutun biyu shi ne, rubutun littafi ya fi  daukar lokaci kasancewar ana yin sa da yawa. domin shi fim za ki iya rubuta fim na daya da na biyua a cikin fallen littafi 60 zuwa 70 amma za ki tarar littafi yakan kunshi daruruwan  shafuka musamamn idan littafin na daya da na biyu har zuwa na uku ne. haka kuma game da daukar lokaci, Littafi ya fi daukar lokaci kafin a kamala. Idan har kina da jigon labarinki a hannu to za ki iya rubuta labarin fim cikin mako guda. Shi kuwa littafi idan har kina da sauri sosai to za ki iya kammala shi cikin sama da watanni uku. Amma duk da haka rubutun labarin fim yana bukatar lokaci musammman idan ba marubuci ne ya kirkiri labarin ba.
Sai dai rubutun littafi ya fi gamsar da marubuci, domin littafi yana fita ne a yadda marubuci yake so, ba kamar na fim ba wanda sai bayan ka rubuta daraktan fim din zai iya cire abubuwan da yake ganin bai yi masa ba ko kuma ya kara abinda yake ra’ayinsa ne. litttafi marubuci yana da ‘yancin rubuta duk abin da ya so, duk kuwa da cewar shi ma yakan hadu da gyare-gyare a wurin mutanen da ka ba su duba maka shi. A wasu lokutan ma sai dai darakta ya zo maka da labarinsa da kansa ya gaya maka abin da yake so a gina labarin fim din akai, kai kuma a matsyainka na marubuci kai za ka kirkiri jaruman fim din da halayyarsu da tarihin rayuwarsu har zuwa karshen abin da ake so a nuna a fim din (Character Profile)
Aminiya: Wane kalubale ake fuskanta game da harkar rubutun fina-finai?
Fauziyya: Shi rubutu abu ne da ke bukatar natsuwa da samun lokaci isasshe. A harkar rubutun fim za ki samu forudusa ya kawo miki aiki amma ke kuma saboda kina tunanin yadda za ki yi rubutun ingantacce sai ki ga har lokacin da kuka ajiye zai karbi aikinsa ya zo amam ke ba ki kamala ba. Saboda shi yana cikin gaggawar ya fita daukar fim dinsa amaikaon ya yi miki uzuri ta hanyar la’akari da dalilanki , amma sai ya nuna bacin ransa game da hakan har ma ya je ya yi ta zaginki cewa kin karbi kudinsa gashi ba ki yi masa aiki ba.
Wata matsalar kuma it ace a wasu lokutan mukan sami matsala da masu fim domin sukan kawo mana wani abin da za mu ga cewa bai kamata ba, ma’ana ya saba da ala’adar Hausawa da abin da yake faruwa a cikin al’umma, to idan muka ga hakan mukan nuna masa aibun hakan. Anan ma maimakin ya fuskanci manufar marubucin sai yaje ya yi ta zagin ka cewa ba ka so ka yi masa aikinsa ne kawai.
Shi kuma littafi matsalar da ake  fuskanta shi ne ta fuskar kasuwanci. Kasancewar littafi ba cinikinsa ake yi a daidai ba, mukan kai wa masu shagunan litattafai da ke kasuwanni da kuma wajen kasuwanni. To za ki samu cewa kin bayar da litattafanki an sayar amma sai kudi su gagara fitowa. Haka za ki yi ta zuwa amam kudin nan da kyar za su fito wasu ma saboda kasancewarmu mata idan ba tsayayye gare ki da zai juri zuwa shagunan masu sayar da litatatfan ba wani lokacin ba za ki sami kudinki ba.
Aminiya: A lokuta da dama akan zargi marubuta da rubuta abubuwan da suka saba wa al’adar bahaushe me yake jawo hakan?
Fauziyya: Kasancewar littafi irin wadanann mun aro su ne daga litattafan Turawa sai ya zama cewar da yawa daga cikin marubuta ba su yin la’akari da bambance-bamnce addini da al’ada da ke tsakaninmu da Turawa ballanatana idan sun tashi su nuna hakan a rubuce-rubucensu.
Da yawa daga cikin marubuta a kokarinsu na son fadakarwa sai suna sakin baki a rubutunsu suna rubuta duk abin da ya zo zuciyarsu.
Kasancewar ba ganinsu ake yi ba sai ki ga wani marubucin ya rubuta abinda bai kamata ba.
Sai dai su ma al’umma a wasu lokutan ba su yi mana adalci, domin idan mutum yana rubutu akan karuwa, ba zai yiwu ka yi ta fadar karuwa a baki ba, dole ne marubuci ya nuna halaye da dabi’un karuwa ta yadda mai karatu zai san cewa wannan karuwar ce da gaske.. kin ga anan dole sai an yi hakuri da marubuci ya nuna wani abin. sai dai  shi kuma marubucin akwai bukatar ya yi duk abin da zai yi da taka tsantasan da alkalaminsa.
Zan yi mafani da wannan damar na yi kira ga ‘yan uwana marubuta da mu rika sanin cewa wannan abu da muke yana iya taba addininmu, domin idan muka rubuta wani abu da bai kamata ba duk wanda ya yi amfani da shi muna da kamashon laifin. Haka kuma a ranar Alkiyama Allah zai tambayi mutum akan abubuwan da ya aikata. A takaice ya kamata mu rika yin la’akari da abin da muke rubutawa. Haka kuma mu rika yin la’akari da irin al’ummarmu da tarbiyyar ‘ya’yanmu a yanayin rubuce-rubucenmu.
Su kuma al’umma ina kira gare su da su rika tsayawa suna yi mana adalci a rubuce-rubucenmu. A wasu lokutan ma wasu ba su karanta littafin amma sai ka ji sun yi kudin goro suna zagin marubuta.
Babu shakka littattanmu suna taka muhimmiyar rawa wajen gyara zamantakewar auratayya. Ta fuskar yadda mace za ta kula da mijinta da tsaftar kanta da gida da gyaran jikin mata. Za ki tarar matan da suke karatun littafi za ki tarar da tsarin rayuwarsu ta bambanta da wadanda ba su yi. Harkar mummunan kishi da asirce-asirce a tsakanin mata yanzu duk sun ragu.
Aminiya: Wane kira kike da shi ga gwamnatia madadin marubuta?
Fauziyya:  To kirana ga gwamnati ta shigo cikinmu tasan abin da muke yi. zan iya cewa a lokacin gwamnatin Shekarau ne kawai aka taba waiwayar marubuta inda har aka dauki wasu marubuta daga cikinmu  aka ba su horo har suka yi rubuce-rubuce don fadakarwa.
Muna so gwamanti ta rika daukar nauyin buga litattafanmu tare da kasuwancinsa. Kamar misalin lokutan baya irin su lokacin Abubakar Imam akwai hukumomin da ke daukar nauyin buga musu litattafansu. To mu ma muna son mu samu hakan. A Haka kuma batun kasuwar litattafan akwai bukatar gwamnati ta shigo cikinmu . muna bukatar gwamnati ta kawo mana wani tsari da za ta taimaka mana wajen yin maganin masu yi mana satar fasaha da kuma masu bayar da hayar litattafanmu. Domin bayar da hayar litattafai yana kasha kasuwancin littafi, idan mutum daya ya sayi littafi daya ya bayar haya sai ki ga mutane sama da 20 sun karanta, to kin ga da ace saye kowannesu zai yi fa?

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited