Kishin yada ilimi da tarbiyya suka sa na zama marubuci – Mustafa Mashi
Monday 26 June 2017     1 Shawwal 1438

Aminiya

A+ A A-

Kishin yada ilimi da tarbiyya suka sa na zama marubuci – Mustafa Mashi

Alhaji Mustafa Abdu Mashi tsohon ma’aikacin kiwon lafiya ne tun daga tsohuwar Jihar Kaduna. An haife shi a 1957 a cikin garin Mashi. Ya yi karatunsa na Firamare a Mashi, sai Kwalejin Gwamnati da ke Katsina. Ya yi karatun karama da babbar diploma a makarantar kiwon lafiya da ke Kaduna. Ya kama aiki da ma’aikatar lafiya tun daga wancan lokaci har zuwa ajiye aikinsa bayan kammala shekaru 35 a matsayin malamin tsabta. Ya bayyana wa Aminiya dalilinsa na fadawa cikin harkokin rubuce-rubucen littattafai a harshen Hausa tun ma kafin ya jiya aikinsa.

Ahmed Kabir S/Kuka, a Katsina

Me ya ja hankalinka ga harkar rubutun littafi kuma a harshen Hausa?
A gaskiya tun kafin in ajiye aiki na fara jaraba rubuta littafi saboda ina da sha’awar abin matuka. To kuma sai karatun wannan jarida ta Hausa wato Aminiya ya kara ba ni kwarin gwiwa sosai a batun karatu ko sanin harshen Hausa. Kuma ina so in yi wani abu a rayuwata wanda zan bar wa baya, don a san ilmin da na yi yana da amfani ga kuma abin da ya haifar. Na farko littafin addini na fara yi a cikin shekara ta 2002, domin dai in bar wani abu wanda na baya za su amfana komai kankantarsa. Bayan na yi wancan littafi sai na ga a’a, bari in kara yin wani. Sai na yi na fannin rayuwa yadda take kasancewa, ba ma kamar ga matasa domin ni littattafaina na matasa ne da hankaltarsu da abin da zai je ya zo da sauransu. Saboda shekarun da na yi ya kamata a ce na samu wani abin da na bar wa baya. Wannan ne ya sa na rubuta littattafan game da gyaran halayyar yaranmu da sauransu.
Ko me ya fado maka a rai a ranar da za ka fara rubuta littafi?
Abin da ya faro fado mani a cikin rai shi ne, tunanin cewa shin wannan abu zai amsu ga jama’a har ya zamo zai amfane su ko kuwa? To sai dai kawai na ce bari in yi, tun da an ce ko yaya ka rubuta kalmar addini, indai har wani ya karu da ita, to kana da lada.
Rubutun littafi yana da dokoki da ka’idoji, yaya ka fuskanci wannan kalubale?
To, ka san komai kake yi akwai na gaba gare ka, kuma in har dai kana son koyon abu, ka je ga masanin abin ka yi tambaya to lallai za ka koyi abin. A hankali ina yi ana kuma tura ni ga wadanda suka fi ni sanin rubutun ma da adabin Hausar gaba daya. Ta haka ne har na gane muhimmancin abin na kuma fara rubutu sosai.
Ka ce ka fara rubutu tun kafin ka ajiye aiki, to mene ne ka karanta wanda ya burge ka har ka shiga rubutun?
Da yake ina da ra’ayin karanta jaridu a duka harsunan biyu, Hausa da Turanci. Wannan ne ya rinjaye ni har na fara tunanin cewa, in dai har za ka fadakar, mutane su karu, lallai ladar da za ka samu ba kadan ba ce. Saboda haka sai nake ganin ba ni so in jefar da basirata ba tare da wani ya karu da abin da na karu da shi ba. Ko kuma abin da wani ya sani, ni in na gani sai in karu da shi, haka na dauki rayuwa.
Ka ce littafin na farko a kan addini ne ka yi shi, ko wane sashe ka dauka na addinin?
To, mafi akasari a lokacin da muke karatu, mukan bar wasu ’yan kura-kurai wadanda kuma su ne matsalarmu. Yanzu kamar wannan wanda na yi, na tambayoyi da amsoshi na yi a kan salloli biyar na farilla. Akwai mutane da yawa wadanda suka ji dadinsa da godiya. Wasu suna cewa dama akwai inda suke so su yi tambaya amma abin ya yi masu nauyi amma wannan littafin ya wadatar da su. To, dama ni irin abubuwan da na yi la’akari da su ke nan. Akwai kura-kuran da mun bar su kuma muna so mu yi tambaya amma kuma muna jin nauyi, amma ta fadakarwa irin wannan in mutun ya karanta sai ya karu, ya kuma warware matsalar.
Ko ka yi tunani a kan matasa, kuma ina ka fi mayar da hankali a wajensu?
To, mafi akasari rayuwa yadda muke gudanar da ita, ba ma kamar al’adunmu na nan Arewa. Mafi akasari in muna da wadata to ba mu damu da mu tarbiyantar da yaranmu su tafi bisa tarbiya ba, sai mu dauko ga ta mu gwada masu wanda kuma yau da gobe ake ji. Ranar da ba ka da rai kuma sai rayuwa ta zo ta canza. Amma in gwargwadon hali ka taimaka, tun da hakki ne Allah Ya dora maka nasu. In ka dauki matakai za a ga an samu canji saboda duk inda ka ga tarbiya koyar da ita aka yi. Ban ce duka ba, amma mafi akasari mu ke bata tarbiyar yaran da kanmu. Kuma in abin ya yi nisa ga lalacewa babu mai iya magana koda ga gaskiyar saboda babba ne ya yi sanadiyar batancin. dan karamin misalin da zan ba da a nan shi ne, sai ka ga yaro tun yana karami ana damka masa kudi. Dubi yadda ake yi wa yara tun daga makarantar reno har zuwa firamare. Maimakon a ba su abinci su tafi da shi makaranta, a’a, koda za a ba su abincin kuma za ka ga ana hada masu da ’yan kudi, wai kudin tara. Ka ga tun daga nan muka fara horon yaranmu da ba su kudi, kuma ka ga wannan bata su yake, domin duk ranar da ba ka ba yaro wadannan kudi ba, to koda ya je makarantar da kyar ne. Kudi suna bata tarbiyar al’umma ma ba yaro ba. To shi ne na ga in dai har za mu dan gyara, to abin zai yi armashi. In muka dan karanta wadannan littattafai, za mu karu da dan wani abu na tarbiyantarwa.
Za mu ci gaba

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited