Media Trust
Monday 26 June 2017     1 Shawwal 1438

Aminiya

A+ A A-

Hukumar Daraktoci

KABIRU A YUSUF, Shugaban Hukumar Daraktoci, Shugaban Kamfani

Tsohon Malamin Jami’a ne, ya yi Editan Jaridar Triumph da Today da Mujallar Citizen, sannan ya taba zama wakilin Kafar Yada labari ta BBC a Kasar Afirka ta Kudu. Ya yi rubuce-rubuce a Mujallar Turanci ta Newswatch da jaridar Daily Times. Ya yi Digirinsa na farko da na biyu kan Kimiyyar Siyasa da nazarin tattalin arziki a Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya da Jami’ar Toronto da ke Kasar Kanada. Kabiru ya yi Manajan-Daraktan, kuma Babban Editan na tsawon shekaru, inda a halin yanzu shi ne shugaban Kamfani.

 

ISIAQ A. AJIBOLA, Manajan Darakta, kuma Jami’in gudanarwa

Kwararre ne a harkar yada labarai. Ajibola ya yi aiki a mujallun Citizen da Sentinel, kuma shi ne Janar-Manajan farko na Kamfanin Media Trust, inda daga bisani ya zama babban darakta (aiwatar da ayyuka), kuma a halin yanzu shi ne Manajan-Darakta, babban jami’in aiwatar da ayyuka. Shi jigo ne a Cibiyar Kwararrun masun kula da amana ta Najeriya (ICTN), kuma tsohon Dalibin Makaranmta koyon harkar kasuwanci da ke KarKashin Jami’ar Stellenbosch, a garin Capetown da ke Afirka ta Kudu. Yana da digirin farko a fannin Tsimi da Tanadi, sannan ya yi digirinsa na biyu kan harkokin kasuwanci da sha’anin mulki (MBA), a Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya dake Najeriya.

 

MANNIR DAN ALI, Babban Darakta, kuma shugaban Editoci

An haife shi a ranar 13 ga watan Mayun 1964 a garin Kayauki dake Jihar Katsina, ya halarci makarantar Firamare ta Ketare da Kankara duk a Jihar Katsina, kafin daga bisani ya samu shiga Makarantar Sakandare ta Kwalejin Rimi da ke Kaduna a shekarar 1976. Ya kuma halarci kwalejin share fagen shiga jami’a ta Zariya, inda bisani ya samu shiga Jami’ar Bayero ta Kano, inda a shekarar 1986 ya samu digirinsa na farko a fannin nazarin harshen Ingilishi. Mannir ya koma Jami’a, ya ci gaba da karatu, har ya samu digirinsa na biyu a fannin Adabin Turancin Ingilishi cikin shekarar 1990. Ya fara aikin jarida ne a Mujallar Citizen, inda ya zama Jami’in kula da ayuka na musamman, daga bisani ya zama wakilinta a Jihar Legas, a tsakanin shekarun 1992 zuwa 1993. Ya kuma yi aikin wucin gadi tare da Sashen Hausa na BBC a shekarar 1994. A tsakanin watan Augustan shekarar 1997 zuwa Fabrairun 2000,. Mannir ya yi aiki da tashar Yada Labarai ta BBC a Hekwatarsu da ke Bush House a birnin Landan, inda daga bisani ya dawo Najeriya, ya bude ofishinsu na Abuja a sashin gudanar da shirye-shiryen Afirka. Ya fara aiki a matsayin Babban Editan Kamfanin Buga Jaridu na Media Trust a shekarar 2007.

 

UMARU ABDULLAHI (Darakta)

Ya yi digirinsa a fannin lissafin shige da ficen kudi, wato Akawun kudi, a Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya. Ya Dan taba aiki a Kamfanin Mai na Kasa, wato “NNPC” kafin daga bisani ya shiga hada-hadar kasuwanci na Kashin kansa. Kwararren mai bayar da shawara ne kan harkokin sarrafa dukiya, wanda ya yi tafiye-tafiye zuwa Kasashen duniya. Alhaji Abdullahi shi ne Manajan Daraktan Kamfanin Hada-hadar Kasuwanci na Intra-Africa International.

 

BELLO DAMAGUM (Darakta)

Babban Dan kasuwa ne, mai hada-hada a Kasashen duniya, ya yi digirinsa a fannin lissafin shige da ficen kudi, wato “Akawun Kudi,” a Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya. Bayan ya yi aiki a Kamfaninm Safarar Jiragen ruwa na Nigeria National Shipping Line, sai ya zama mai kamfanin gina gidaje da kasuwancin gidaje da filaye a Abuja da Kaduna.

 

ABDULLAHI SHUAIBU (Darakta)

Shugaban Kamfanin Sayar da Motoci da Kayan aikin gona na Agromatrix Nigeria Limited. Ya yi digirinsa a fannin Kasuwanci da Sha’anin Mulki a Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya, sannan ya dade yana aiki tsawon shekaru a Kamfanin motoci na SCOA Nig. Ltd, a sassa daban-daban na Kasar nan.

 

RABIU GARBA (Darakta)

Shi ne Shugaban Kamfanin Dab’i / Manajan Daraktan Espee Printing & Advertising Limited. Ya yi Babbar Difuloma (HND) a fannin Fasahar Dab’I a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kaduna.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited