An kama jami’an Hukumar Zaven Ghana
Monday 26 June 2017     1 Shawwal 1438

Aminiya

A+ A A-

An kama jami’an Hukumar Zaven Ghana

Hukumar Zaben kasar Ghana ta tabbatar da kama wasu jami’anta biyu bayan da aka zarge su da laifin cire sunayen wasu ’yan takara daga rijistar masu zabe.

Hukumar zaben kasar, ta tabbatar da cewa an cire sunan Dokta Bawumia ne a wajen wurin baje rijistan masu zaben, abin da kamar yadda ta ce, ya saba ka’idodinta.
Hakazalika, ta samu jami’anta biyu da laifin karya ka’idodinta kuma ta ce har ta sallame su.
A wani jawabi da mukaddashin shugaban  hukumar wadda ke kula da ayyuka Mista Amadu Sulley ya gabatar ya ce wani kwamitin mutum uku da hukumar ta kafa don binciken lamarin ya gano cewa jami’an zaben sun karya ka’idodin hukumar ta duba sunan Dokta Bawumia.
Jawabin ya ce kwamitin ya tabbatar da cewa jami’an biyu Mista Ambrose Yobe da Mumuni Latifa sun tashi aiki gabanin lokacin tashinsu.
Haka kuma sun taimaka wa Dokta Bawumia wurin baje rajistar a cibiyar zabe. A kan haka ke nan sun kauce wa ka’idodin hukumar zaben, kamar yadda jami’in ya bayyana.
Sai dai jawabin ya ce hukumar kadai ce, take da hurumin bayyana inda za ayi wanna atisaye.
Ya ce jami’an da ke aikin, ba su da wani ikon zaban wani wuri ba tare da izinin hukumar zaben ba.
A karshe hukumar ta ja hankalin ’yan siyasa kan su dukufa wajen sanin dokokin da ka’idodin zabe saboda yadda hakan zai taimaka musu sanin abin da ya dace ayi da wadanda ba su dace ba.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited