Za a bude otel mai fi girma a duniya a Makkah
Monday 26 June 2017     1 Shawwal 1438

Aminiya

A+ A A-

Za a bude otel mai fi girma a duniya a Makkah

A shekara mai zuwa ne ake saran bude wani sabon otel a birnin Makkah na kasar Saudiyya, kamar yadda jaridar Biritaniya ta The Independent ta bayyana.

Ma’aikatar Kudi ta kasar Saudiyya ce dai take daukar nauyin aikin, wanda wani kamfanin mai zaman kansa mai suna Dar al-Handasah yake gudanarwa.
Katafaren otel din yana da nisan Kilomita biyu kacal daga Masallacin Harami, wanda yake daukar masu ibada akalla mutane biliyan biyar kowace shekara, a lokutan aikin hajji da kuma umarah.
Wani rahoto ya ce idan aka kammala ginin za a ware wa gidan sarautar Saudiyya hawa guda biyar a benen.
Otel din zai kunshi dakuna dubu 10 da wuraren cin abinci guda 70, kuma girmansa zai kai murabba’in mita miliyan daya da dubu 400.
Har ila yau, akwai wasu rahotanni da suke cewa aikin ginin zai ci kimanin Fam biliyan biyu da miliyan 700 (wato fiye da Naira Tiriliyan daya ke nan).

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited