An samu jinkiri wajen jigilar mahajjatan Nijar
Saturday 24 June 2017     29 Ramadan 1438

Aminiya

A+ A A-

An samu jinkiri wajen jigilar mahajjatan Nijar

A jamhuriyar Nijar an samu jinkiri wajen fara jigilar mahajjata zuwa kasar Saudiyya, domin gudanar da aikin hajjin bana.

A ranar Talata da daddare ne yakamata ace jirgin farko dauke da maniyyatan zuwa Saudiya, amma hakan bai yi wu ba.
Hukumar hajji da umara ta kasar COHO ta ce matsalar ta samo tushe ne daga kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na Niger Airways, wanda shi ne aka ba kwangilar jigilar maniyyatan sai dai bai samu jirgi ba, kamar yadda BBC ta bayyana.
Kimanin maniyyata 12,712 ne za su tafi aikin hajji bana daga Nijar.
Hukumar tsare-tsaren hajjin na sa ran kammala jigilar maniyyatan a ranar 31 ga watan nan.
A makon jiya ne aka fara jigilar mahajjatan makwabciyarta Najeriya, inda aka da maniyyatan Jihar Zamfara wadanda suka tashi daga shiyyar Sakkwato.
Kimanin maniyyata hajjin kusan dubu 58 ne daga jihohi za su isa kasa-Mai-Tsarki a bana, sai alhazai 8500 daga kamfanoni masu zaman kansu.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited