Za a sallami fursunoni dubu 38 a Turkiyya
Saturday 24 June 2017     29 Ramadan 1438

Aminiya

A+ A A-

Za a sallami fursunoni dubu 38 a Turkiyya

Gwamnatin kasar Turkiyya ta ce za ta saki mutane dubu 38 da ke zaman gidan kaso a wani mataki na gyara halin ka, kamar yadda kafar yada labarai ta BBC ta bayyana.

Duka wadanda za a saki din dai wadanda aka yankewa hukunci ne gabanin yunkurin juyin mulkin watan jiya.
Sai dai daga cikin mutanen da aka yi wa afuwar ban da wadanda aka yankewa hukunci sabo da laifukan kisan kai da fyade da kuma ta’addanci.
Gwamnati dai ba ta ba da dalilin yin afuwar ba, to amma wasu na ganin mai yuwawa gwamnatin ta yi haka ne domin ta samu sararin da za ta kulle dubban mutanen da aka kama bayan yunkurin juyin mulkin da bai yi nasar ba a tsakiyar watan jiya.
Haka kuma gwamnatin ta kafa wata doka da a karkashinta aka kori fiye da ‘yan sanda dubu biyu da kuma daruruwan sojoji bisa zarginsu da hannu a yunkurin juyin mulkin. Hakazalika, an kuma kori jami’ai da dama daga kamfanin sadarwan kasar.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited