Shugaban Ghana ya yi wa ma’aikatan rediyo afuwa
Friday 28 July 2017     4 Zulki'da 1438

Aminiya

A+ A A-

Shugaban Ghana ya yi wa ma’aikatan rediyo afuwa

Shugaban kasar Ghana John Mahama ya yi wa ma’ikatan gidan rediyon nan guda uku afuwa bisa tuhumar su da yin barazanar ga wasu alkalan kasar.

A ranar 27 ga watan jiya ne Babban Kotun Ghana ta daure ma’aikatan MUNTIE FM wata hudu, tare da cin su tarar GHc10,000 ko wane dayansu, saboda kotun ta same su da laifin yi wa alkalan kotun barazanar kisa.
Bayan hukuncin,magoya bayan jam’iyya mai mulki NDC sun matsawa Shugaba Mahama kan ya yi amfani da ikon da kundin tsarin  mulki kasar ya ba shi na yi wa mutanen uku afuwa wato Salifu Maase da Alistair Nelson da kuma Godwin Ako-Gunn.
Daga nan sai Shugaba Mahama ya mika takardan koken da  aka bashi ga majalisar dattawan kasar don su ba shi shawara a kan lamarin. Hakan ya a a ranar Litinin kwasam shugaban bisa shawaran majalisar dattawan, ta yi wa mutane ukun afuwa wato za su yi wata uku ne a gidan yari, maimakon wata hudu da aka yi musu tun farko.
Wannan ya jawo kace-na-ce, wasu na suka, wasu kuwa suna jinjina wa shugaban musanman magoya bayan jam’iyyar NDC.
Darektan zantarwan Media Foundation for West Africa Sulemana Braimah yac e wannan abin da shugaba ya yi abin damuwa ne ga kasar, saboda zai ba mutane damar fadan duk abin da suka ga dama kan rediyo don sun yi imani shugaban kasa zai tsaya musu.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited