An kama masu amfani da WhatsApp a Burundi
Friday 28 July 2017     4 Zulki'da 1438

Aminiya

A+ A A-

An kama masu amfani da WhatsApp a Burundi

‘Yan sanda a kasar Burundi suna ci gaba da tsare mutane tawkas da ake zargin da bata sunan gwamnati a dandalin sada zumunta na WhatsApp.

An cafke wadanda ake zargin ne a lokacin da suke wata ganawa wanda ‘yan sanda suka ce ta kitsa yadda za su kara yada labaran karya ne.
Tun a bara ne dai aka fara samun rudani a kasar, lokacin da mummunan tashin hankali ya barke saboda neman sake tsawaya takara a karo na uku da Shugaba Pierre Nkurunziza ya yi.
Masu sukar gwamnatin Burundi sun ce cafke mutanen takwas wani mataki ne na takaita ‘yancin yada bayanai a kasar.
Amma kuma mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda ya zargi ‘yan kungiyar ta Whatsapp da haddasa mummunan tashin hankali bara a kasar.
Ya ce za dauki tsauraran matakai kan mutanen da ke yada jita-jita a shafukan sada zumunta.
Shafukan sada zumunta sun kasance wasu hanyoyin da suka fi yin fice wajen samun labarai, bayan da aka rufe gidajen rediyo da dama  bara a kasar.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited