Sojin Turkiyya sun kutsa Siriya
Saturday 24 June 2017     29 Ramadan 1438

Aminiya

A+ A A-

Sojin Turkiyya sun kutsa Siriya

 Motocin yaki na kasar Turkiyya sun nausa zuwa cikin kasar Siriya domin korar mayakan kungiyar masu ikirarin kafa Daular Musulunci ta IS daga yankunan iyakar kasarta.

Gabannin hakan an yi barin wuta a kan wuraren da ke hannun ‘ya’yan kungiyar.
Wasu majiyoyin sojin Turkiyyar sun shaida wa kafafen yada labarai na kasar cewa, harin ya lalata wurare 70 a Jarablus, yayin da wani harin ta sama ya lalata wasu wuraren 12.
‘Yan tawayen Siriya da ke samun goyon bayan Turkiyya na rufawa dakarun kasar baya a harin.
Turkiyya ta ce kutsen da ta yi cikin Siriya ba kawai tana harin ‘yan IS ba ne, har ma da mayakan kurdawa da ke dauke da makamai.
A ranar Lahadin da ta gabata ne akalla mutane 30 suka rasu wasu 90 suka ji mummunan rauni, a lokacin da wani bam ya tashi a wurin bikin aure a Jihar Gaziantep da ke kudu masu gabashin kasar.
Mataimakin Firaministan kasar Mehmet Simsek, ya ce harin ya yi kama da na kunar bakin wake.
Manyan motocin daukar marasa lafiya ne suka cika wurin da aka kai harin wanda ya ke tsakiyar jihar.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited