Kotun Amurka ta ba dalibai damar daukar bindiga
Monday 26 June 2017     1 Shawwal 1438

Aminiya

A+ A A-

Kotun Amurka ta ba dalibai damar daukar bindiga

Wata kotu a kasar Amurka ta ce daliban Jami’ar Tedas za su iya ci gaba da shiga da bindiga ajujuwan daukar darasi da ke makarantar.

Kotun ta yanke wannan hukuncin ne bayan wadansu malaman jami’ar su uku wato Dokta Jennifer Lynn Glass da Dokta Lisa Moore da kuma Dokta Mia Carter sun shigar da hukumomin jami’ar da gwamnatin Jihar Tedas kara a gabanta bisa kalubalantar matakin bai wa daliban damar shiga da bindiga ajujuwa yayin daukar darussa, kamar yadda kafar yada labarai ta KdAN ta bayyana.
Masu gabatar da karar sun ce matakin yana tattare da hadari, inda suka ba da misalin hare-hare akalla guda 20 da ya faru a manyan makarantun kasar a bara.
Bayan kammala zaman kotun Babban Lauyan Gwamnatin Jihar Ken Padton ya ce: “Ina cikin farin ciki, amma ban yi mamaki ba kan yadda kotun ta ki amincewa da bukatar hana amfani da bindiga a makarantu. Babu wata doka da ta hana dalibai daukar bindiga don su kare kansu.”
“Doka ta bai wa kowane Ba’amurke damar mallakar makamai ciki har da daliban manyan makarantu. Kuma a kowane lokaci a shirye nake in kare wannan ’yancin,” inji shi.
A watan jiya ne hukumomin makarantar suka bai wa dalibai damar daukar bindiga a cikin jami’ar don su kare kansu idan bukatar hakan ta taso.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited