An sallami na’iban limamai dubu 10 a Saudiyya
Saturday 24 June 2017     29 Ramadan 1438

Aminiya

A+ A A-

An sallami na’iban limamai dubu 10 a Saudiyya

Ma’aikatar Harkokin Addinin Musulunci ta Saudiyya ta sallami na’iban limamai guda dubu 10 domin tsuke bakin aljihu.
Ta ce matakin zai sa a yi tsimin Riyal miliyan 360.
An baiwa na’iban limaman zabin, ko su zama cikakkun limamai su rika gabatar da salloli biyar, ko kuma su nemi wata sana’ar, kamar yadda jaridar Saudi Gazette ta bayyana.
Wasu dai na sukar na’ibai a kasar, inda suke cewa akasari ba sa yin aikin komai, kuma suna karbar albashin Riyal 3000 kowane wata.
Sai dai wasu a kasar sun koka cewa, sallamar na’iban daga aiki zai haifar da karancin limamai da za su rika jagorantar salloli biyar.
Masu wannan korafi sun ce, za a samu matsala a duk lokacin da limamai suke hutunsu na shekara-shekara.
Gwamnatin Saudiyya tana shirin rage kudaden da take kashewa saboda tasirin faduwar farashin mai, wanda shi ne babban jigon gudanar da gwamnatin kasar.
A bara Ministan kudi, Ibrahim Alassaf ya ce wasu manyan ayyuka da tuni aka amince da yinsu, yanzu za a dakatar da su.
Duk da cewa bai ba da cikakken bayani a kan wuraren da tsuke bakin aljihun zai shafa ba, amma ya ce lamarin ba zai shafi bangaren kiwon lafiya da ilimi ba.
Hukumomin Saudiyya sun yi hasashen cewa za su fuskanci gibin dala biliyan arba’in a kasafin kudin bana, amma masana sun ce gibin ya wuce haka nesa.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited