An tsige Shugabar Brazil
Saturday 24 June 2017     29 Ramadan 1438

Aminiya

A+ A A-

An tsige Shugabar Brazil

Majalisar Dattawan kasar Brazil ta tsige Shugabar kasar Dilma Rousseff bayan samunta da laifin yin amfani da kasafin kudin kasar don cimma bukatun kashin kanta.
Matakin ya kawo karshen mulkin jam’iyya Workers’ Party wadda ta shafe shekara 13 tana mulki. Sai dai ta musanta  duka zargin da ake mata.
A shekaranjiya Laraba ne ’yan Majalisa 61 suka kada kuri’a tsige ta, yayin da guda 20 suka kada ta rashin amincewa da matakin.
Hakan yana nufin Mukaddashin Shugabar kasar Michel Temer zai karasa wa’adinta wadda zai zo karshe a ranar 1 ga watan Janairu shekarar 2019.
Tun da farko dai Shugaba Rouseff ta bukaci kotun kolin kasar ta dakatar da yunkurin tsigeta, abin da ya ci tura.
Shugabar Brazil da ke fama da fadi tashin siyasa, ta musanta zargin da ake yi mata na yin amfani da kasafin kudi lokacin zabe.
An dai dakatar da ita daga mukamin ta ne a watan Mayun bana.
Sauran zargin da ake wa shugabar sun hada da daukar bashi a bankunan kasar da nufin cike gibin kasafin kudin kasar na shekarar 2014.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited