Ali Bongo ya lashe zaben Gabon
Friday 28 July 2017     4 Zulki'da 1438

Aminiya

A+ A A-

Ali Bongo ya lashe zaben Gabon

Hukumar Zaben kasar Gabon (Cenap) ta bayyana Shugaba Mai Ci Ali Bongo a matsayin wanda ya lashe zaben kasar da fiye da kaso 49 cikin 100 na kuri’un da aka kada ranar Lahadi, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya bayyana.
Jami’an tsaro a kasar suna sintiri a titunan babban birnin kasar Librabille, gabani da kuma bayan bayyana sakamakon zaɓen shugaban kasar da aka gudanar a karshen mako.
Tun da farko dai Shugaba Ali Bongo da kuma babban abokin adawarsa, Jean Ping duka sun yi ikirarin samun nasara a zaben.
Sakatare Janar na Majalisar dinkin Duniya, Ban Ki-Moon ya yi mgana da dukkansu biyu ta waya domin kwantar da hankulla.
Ban Ki Moon ya bukaci ‘yan siyasar biyu su yi kira ga magoya bayansu su kwantar da hankali yayin da ake jiran sakamakon zaben.
Ali Bongo, da mahaifinsa marigayi Omar Bango sun kwashe kusan shekara 50 suna mulkin kasar ta Gabon.
kasar wadda take yammacin Afirka tana jama’a kimanin miliyan daya da rabi. Ta samu ’yancin kai ne daga Turawan Faransa a shekarar 1960. Kuma tattalin arzikinta ya dogara ne kacokan ga man fetur.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited