Donald Trump ya ziyarci Medico
Monday 26 June 2017     1 Shawwal 1438

Aminiya

A+ A A-

Donald Trump ya ziyarci Medico

dan takarar shugabancin Amurka na jam’iyyar Republican, Donald Trump ya ziyarci kasar Medico shekaranjiya Laraba.
Wannan dai yana zuwa ne ‘yan sa’o’i kafin dan takarar ya fitar da wasu matakan da yake ganin zai dauka, idan ya ci zabe, kan ‘yan cirani a wani jawabi da ya gabatar.
Mista Trump ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa yana son yin ido-biyu da Shugaban Medico Enrikue Pena Nieto wanda ya gayyace shi da Hillary Clinton.
Donald Trump ya soki ‘yan cirani ‘yan kasar Medico da ke Amurka, a lokacin yakin neman zabensa, inda ya sha alwashin gina katanga tsakanin kasashen biyu.
dan takarar yana ci gaba da samun koma baya a zaben jin ra’ayoyin jama’a tun bayan babban taron jam’iyyarsa a watan Yuli, yayin da abokiyar hamayyarsa Hillary Clinton take kan gaba musamman tsakanin al’ummar Amurkawa marasa rinjaye.
Shugaban Medico ya ce ya gayyaci duka ’yan takarar biyu don ganawa da su. “Hanyar maslaha ce za ta kare manufofin kasar Medico a duniya,” inj shi.
Sai dai zuwa yanzu Misis Clinton ba ta bayyana karbar goron gayyatar shugaban ba tukuna.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited