Harkokin kasuwanci sun fara farfadowa a Fotokol
Saturday 24 June 2017     29 Ramadan 1438

Aminiya

A+ A A-

Harkokin kasuwanci sun fara farfadowa a Fotokol

Bayan samun wanzuwar kwanciyar hankali a garin Fotokol da yake kan iyaka kasar Kamaru da Najeriya, harkokin kasuwanci sun fara farfadowa.
Hakan ya biyo bayan takaita kai hare-haren ta’addanci da kungiyar Boko Haram ta dinga rubanya kai wa a garin.
Lamarin da ya sa motocin safara suka fara sake yin kai kawo tsakanin Kousseri da kuma Fotokol. Hakan bai hana jama’a rayuwa a cikin wani hali na dar-dar ba, ganin cewa lokaci-lokaci kungiyar Boko Haram ta kan kai hare-hare a wasu wurare.
Sai dai gwamnati ba ta saki jiki da wannan samun dan kwanciyar hankalin da aka yi ba a garin.
Hakan ya tabbata ne bayan rufe makaratun boko fiye da 181 da ta yi a aukacin lardin Arewa-mai-Nisa lokacin da a mako mai zuwa wato ranar 6 ga watan Satumba za a koma makarantu zagon shekarar 2016/2017 a duk fadin kasa.
A fadin ma’aikatun kula da ilimin yara kanana da kuma na ilimin sakandare suka ce kashi 69 na daukacin makarantun da aka rufe, an yi musu barazana ko kuma an kai musu hari.
Abin da ya danganci karamar Hukumar Fotokol, makarantu 22 aka rufe. Wannan lamari kuma zai shafi harkar ilimi a yankin da tun farko yake fuskantar matsalar aika yara makarantu.
Ana cikin tuna yadda za a yi wurin warware wannan matsala kuma, sai ga shi Ministan Ilimi Sakandare ya fidda wata sanarwa inda ya nemi daraktocin makarutu da su bi umarnin daidaita adadin dalibai a aji na farko na sakandare a 60. Sauran ajujuwan kuma a tsaya a dalibai 80.
Wannan a makarantun gwamnati ke nan. Sai dai halin da ake ciki a yanzu shi ne, tarin iyayen yara na fuskantar matsalar rashin isashen kudade na biya wa yaransu karatu a makarantu masu zaman kansu. A dalilin haka ne masu yara 4 zuwa sama suke son ganin cewa yaran nasu sun samu shiga makarantun gwamnati, inda kudin da ake biya ba shi da yawa.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited