Zaben Gabon: Bongo ya zargi EU da nuna son kai
Saturday 24 June 2017     29 Ramadan 1438

Aminiya

A+ A A-

Zaben Gabon: Bongo ya zargi EU da nuna son kai

Shugaban kasar Gabon Ali Bongo ya zargi masu sa ido na kungiyar Tarayyar Turai da nuna son kai bayan da suka bayyana cewa an tafka kura-kurai a zaben Shugaban kasar da aka bayyana Bongo a matsayin wanda ya yi nasara.
A ranar Talata ne Ministan Shari’ar kasar, Seraphim Moundounga ya yi murabus, yana fargabar cewa kasar na iya fadawa cikin rikici sakamakon gardamar da ta biyo bayan zaben.
An dai yi ta yin gargadi game da sahihancin sakamakon zaben, gabanin daukar matakin yin murabus dinsa.
Sai dai Ministan Watsa Labarai na kasar, Alain Claude Billy, ya ce murabus din Mista Seraphim bai ba shi mamaki ba, kuma Shugaba Bongo zai ci gaba da mulki. Ya kuma zargi shugaban jam’iyyar hamayya Jean Ping da yin magudi.
bangaren adawa dai ya ce an tafka magudi a zaben.
Ana dai sa ran kotun tsarin mulki za ta yi zama domin sauraron karar da Mista Ping ya shigar a gabanta wanda ke kalubalantar sakamakon zaben.
Mista Bongo ya ce zai bai wa kotun hadin kai idan har ta bukaci a sake kidaya kuri’un da aka kada.
A ranar Litinin Mista Ping ya bukaci a fara yajin-aiki a kasar baki daya, saboda a cewarsa an kashe ’yan adawa da dama a rikicin da ya biyo bayan zaben.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited