Shugaban Philippines ya nemi gafarar Obama
Monday 26 June 2017     1 Shawwal 1438

Aminiya

A+ A A-

Shugaban Philippines ya nemi gafarar Obama

Shugaban kasar Amurka Barack Obama ya ki ganawa da Shugaban Philippines Rodrigo Duterte, yayin da yake halartar taron kungiyar kasashen Kudu-maso-Gabashin Asiya saboda abin da ake ganin kalaman batanci da aka yi masa.
Fadar Shugaban Philippines ta fitar da sanarwa inda take janye kalaman batanci da Shugaban ya yi.
Da farko an shirya shugabannin biyu za su gana a wajen wannan taro da ake yi a bietiane babban birnin Lao, inda shugabannin kungiyar ke taronsu na shekara-shekara don karfafa dankon zumuncin da ke tsakaninsu, kamar yadda rediyon Faransa (RFI) ya bayyana.
Sai dai kuma taron na bana babu armashi saboda sabanin da ke tsakanin Amurka da Philippines, wadanda sun dade suna zumunci, kafin abin ya kai ga Shugaban Philippines ya yi ta ruwan ashar kan Shugaban Amurka a dan tsakanin nan. Jami’an Amurka sun bayyana cewa taron da aka shirya na shugabannin kasashen biyu an soke saboda kalamai na baya-bayan nan da Shugaban Philippines ya rika yi cewa Obama dan karuwa ne.
Shugaban Philippines ya fadi cewa zai kara barota muddin Shugaban Amurka ya nemi tursasa masa game da kisan da ake yi wa masu mu’amala da miyagun kwayoyi a kasar.
A bana ne aka zabi Shugaba Rodrigo Duterte da kuri’u masu rinjaye, kuma zuwa yanzu akalla mutum 3000 aka kashe saboda mu’amula da miyagum kwayoyi, ma’ana tun hawansa shugabanci duk rana akan kashe akalla mutum 44 don yaki da miyagun kwayoyi.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited