Saudiyya ta maida martani ga Iran kan aikin hajji
Saturday 24 June 2017     29 Ramadan 1438

Aminiya

A+ A A-

Saudiyya ta maida martani ga Iran kan aikin hajji

kasar Saudiyya ta mayar da martani mai zafi kan kalaman Shugaban Addini na kasar Iran Ayatullah Ali Khamenei, inda ya ce Musulumin duniya su kalubalanci yadda Saudiyya take gudanar da ayyukan Hajji.
Khamenei ya bayyana matakin Shugabannin Saudiyya a matsayin abin “kunya da rashin hankali” kan yadda suke kama-karya kan harkokin addini.
Shugaban addini ya bukaci kasashen Musulmi su tuhumi Saudiyyar kan yadda take kula da Masallatan Makkah da Madinah da kuma yadda take tursasa wa bakin Allah.
Shugaban Malaman Saudiyya, Aldul’aziz Al-Sheikh ya bayyana Iraniyawan a matsayin wadanda ba Musulmi ba, saboda yadda suke kyamar Saudiyyar da mabiya Sunnah, kamar yadda rediyon Faransa (RFI) ya bayyana.
A nasa bangare, Yarima mai jiran gado Mohammed bin Nayef ya ce, Saudiyya ta dauki duk matakan da suka dace wajen kare lafiyar mahajjata da inganta jin dadinsu ta hanyar samar musu da masaukai na zamani da kuma tsaro.
Nayef ya ce, sun ki amincewa da bukatar Iran na gudanar da zanga-zanga a lokacin aikin Hajji, daya daga cikin dalilan da suka hana mahajjantan kasar zuwa aikin Hajjin bana.
Alhazan Iran 464 suka mutu a hadarin bara, kuma ga alama cacar baki tsakanin bangarorin biyu ba za ta kau ba.
A karon farko cikin shekara 30 an Iran ta ki tura mutanenta aikin Hajji bayan gaza cimma daidaito a tattaunawar tsawon lokaci kan batun tsaron mahajjata.
Iran na ci gaba da bayyana takaicinta kan turmutsitsi Hajjin bara da ya yi sanadiyyar rasa rayukan alhazai 2,300, wadanda 464 ’yan kasar Iran ne, kamar yadda kasar take ikirari.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited