Amurka ta yi Allah-wadai da harin Afghanistan
Monday 26 June 2017     1 Shawwal 1438

Aminiya

A+ A A-

Amurka ta yi Allah-wadai da harin Afghanistan

kasar Amurka ta yi Allah-wadai da kakkausar murya kan munanan hare-haren baya-bayan nan da aka kai birnin Kabul na kasar Afghanistan, inda aka kashe tare da raunata dimbin jami’an tsaro da farar hula.
kasar ta bai wa Afghanistan tabbacin cewa za ta hada kai da ita don tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali da kuma ci gaban kasar.
Tuni kungiyar Taliban ta dauki alhakin kai wadannan hare-hare.
Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka Mark Toner ya fadi a ranar Talata cewa Amurka za ta ci gaba da tattaunawa da Afghanistan da Pakistan domin kakkabe harkokin ta’addanci a kasashen biyu, kamar yadda gidan rediyon Muryar Amurka (bOA) ya bayyana.
Tagwayen hare-haren kunar bakin waken da aka kai wuri mai cike da hada-hada a Kabul, su ne na farko a jerin hare-haren na ranar Litinin, sai wani harin da aka kai da mota ’yan sa’o’i bayan nan a wani wurin da ke daura da ofisoshin gwamnati da na diflomasiyya. Daga nan kuma wasu ’yan bindiga su uku su ka ja daga daura da wani ginin gwamnati wanda ke kusa da ginin wata kungiyar agaji, da ake kira Care International, wanda aka yi kaca-kaca da shi.
Wani jami’in gwamnatin Afghanistan ya ce jami’an tsaro sun hallaka dukkan ’yan bindiga ukun wanda ya kawo karshen mamayar ta tsawon sa’o’i a cikin dare.
Tun da dadewa gwamnatin Afghanistan ke zargin kasar Pakistan, musamman ma cibiyoyin sojinta da goyon bayan ’yan tawayen Taliban a asirce a Afghanistan.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited