Ana zargin wasu ‘yan mata da alaqa da IS
Monday 26 June 2017     1 Shawwal 1438

Aminiya

A+ A A-

Ana zargin wasu ‘yan mata da alaqa da IS

An kama wasu ‘yan mata huxu ‘yan qasar Faransa da ake zargin suna shirya aikata ta’addanci.
Kafar yaxa labaran Faransa ta ce ‘yan matan na tsakanin shekara 14 ne da 18, kuma an kama su suna bin Rachid Kassim, wani xan qasar da ke cikin mayaqan qungiyar IS, wanda kuma ya qware da baiwa mayaqan horo kan dabarun yaqi, suna musayar bayanai da ‘yan matan ta kafar sadarwar Intanet.
Ko a farkon wannan watan jiya jiragen yaqin Amurka marasa matuqa sun kusan kai hari a mavoyarsa.
Masu gabatar da qara sun ce ‘yan matan sun tattauna kan yadda za su tada zaune tsaye, da haddasa fitina.
Kuma ta yi wu sun fara shirye-shiryen yin balaguro zuwa qasar Siriya ko Iraqi wato qasashen da ake kallon su a matsayin cibiyar qungiyar IS.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited