An hana sayar da Coca-Cola a Indiya
Saturday 24 June 2017     29 Ramadan 1438

Aminiya

A+ A A-

An hana sayar da Coca-Cola a Indiya

‘Yan kasuwa a garin Tamil Nadu da ke kudancin Indiya sun hana sayar da lemun Koka-kola da Pepsi domin a riqa sayen lemun da ake haxawa a cikin gida.
A ranar Laraba ne dai aka fara daina sayar da lemun waxanda manyan qungiyoyin ‘yan kasuwan biyu suka bayar da shawarar a hana sayensu.
Qungiyoyin sun ce kamfanonin da suke samar da irin waxannan lemun na amfani da ruwa mai yawa daga koguna.
Hakan kuma yana sa manoma suna shan wahala wajen ban ruwa a gonankinsu a lokutan da ake fama da matsanancin fari.
Qungiyar yin lemu ta Indiya, IBA, ta ce ba ta ji daxin matakin da aka dauka ba.
Qungiyar IBA, wadda ke wakiltar akasarin kamfanonin da ke yin lemun kwalba, ta ce hanin da aka yi “ya sava wa shika-shikan ci gaban tattalin arziki”.
Kamfanin Coka-Cola da na Pepsi da ke qasar sun samar wa iyalai dubu biyu aikin yi kai tsaye a garin Tamil Nadu.
Yayin da a hannu guda kuma ya samar wa wasu iyalan dubu biyar ayyuka a wasu vangarorin kamfanin.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited