Trump ya zargi Obama da shirya zanga-zanga
Saturday 24 June 2017     29 Ramadan 1438

Aminiya

A+ A A-

Trump ya zargi Obama da shirya zanga-zanga

Donald Trump 3Shugaban Amurka Donald Trump ya ce, ya yi amanna cewa Barack Obama na da hannu wajen shirya zanga-zangar nuna adawa da ’yan majalisar dokokin qasar qarqashin Jam’iyyar Republican da kuma fallasa bayanan sirrin fadar White House.
A wata hira da ya yi da kafar yada labarai ta FOX, Shugaba Trump ya ce, “ Ina tunanin Shugaba Obama na da hannu cikin wannan lamari saboda mutanensa na da hannu.”
Trump ya qara da cewa, akwai kuma siyasa a cikin lamarin amma bai ba da wata hujja ba dangane da iqirarin nasa. ’Yan Majalisar na Republican na shan tambayoyi daga al’ummar da ta zabe su dangane da tsarin tafiyar da mulkin Trump.
Kawo yanzu dai tsohon shugaban na Amurka Barack Obama bai mayar wa Trump da martani ba kan batun.
Hirar da aka yi da Trump dai ta zo ne ’yan sa’o’i gabanin jawabin da zai gabatar a gaban zaman haxin gwiwa na majalisun qasar biyu, in da ake saran zai ba da cikakken bayanai game da shirinsa na taqaita kashe kudi da kuma habbaka tattalin arzikin Amurka.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited