An rantsar da Amina Muhammad
Monday 26 June 2017     1 Shawwal 1438

Aminiya

A+ A A-

An rantsar da Amina Muhammad

An rantsar da Amina MuhammadAn rantsar da tsohuwar ministan muhallin Najeriya Amina Muhammed a matsayin Mataimakiyar Sakatare Janar ta Majalisar Xinkin Duniya a birnin New York ranar Talata.
Sakatare Janar Antonio Guterres ya rantsar da ita, bayan naxin da ya mata a watan jiya.
Amina Muhammed ita ce mace ta biyu da za ta riqe wannan muqamin bayan Asha-Rose Migiro ’yar qasar Tanzaniya da ta riqe muqamin a qarqashin Ban Ki Moon tsakanin shekarar 2007 zuwa 2012. Sai dai Amina ta maye gurbin Jan Eliasson na qasar Sweden qarkashin shugabancin Ban Ki-Moon.
Ana ganin Amina za ta taka muhimmiyyar rawa na kawo sauyi da zai qunshi daidaito musanman ’yancin mata.
Amina Muhammed ta riqe muqamin ministar Muhalli a Najeriya kafin zama mataimakiyar sakatare janar na Majalisar Xinkin Duniya.
Wannan muqami da Amina ta samu ya biyo bayan kashi 75 cikin 100 na qasashen Majalisar Xinkin Duniyan da suka yi maraba da surka mata cikin manyan kujerun gudanarwa a majalisar.
Amina wadda za ta riqa wakiltar Babban Sakataren Majalisar ta fuskar diflomasiya a duniya ta ce za ta yi amfani da matsayinta wajen qara farfaxo da martabar Najeriya da Afirka da kuma Musulunci.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited