Yadda yara ke amfana da citta a Kafanchan
Tuesday 27 June 2017     2 Shawwal 1438

Aminiya

A+ A A-

Yadda yara ke amfana da citta a Kafanchan

Garin Kafanchan da ke karamar Hukumar Jama’a ita ce cibiyar kasuwancin citta a yankin Kudancin Jihar Kaduna. Duk da cewa kananan hukumomin Kachiya da Kagarko da Jaba su suka fi ko ina noma citta ba kawai a Kudancin Jihar Kaduna ba, hatta a kasar baki daya.
Bayan manoma daga wadannan kananan hukumomin da muka ambata sun nome cittar, sai masu saye daga garin Kafanchan su fara sayowa cikin manya da kananan motoci suna kawowa Kafanchan don gyarawa. Ko da cikin tirela aka sayo sai an juye gaba daya an yi tsinta da shika wanda samari da kananan yara, maza da mata da tsofaffi ke aikin yi ana biyansu. A irin wannan lokaci kusan kowa na da aikin yi kama daga masu tsinta da shika, zuwa masu durawa da dinkewa, har zuwa direbobin da ke kwasowa daga kauyuka baya ga masu aikin dako da lodi.
Har ila yau, baya ga masu zuwa sayen cittan da suke zarcewa kai-tsaye zuwa ga manoman don saya zuwa garuruwansu musamman ’yan koli, sauran manyan ’yan kasuwa da kamfanoni na ciki da wajen Najeriya da suka hada da kasashen Indiya da Pakistan da Amurka da Sudan da Chadi da sauransu sukan bayar da aikin ne ga manyan dillalan da ke daukan nauyin saye da gyarawa da kuma lodawa zuwa garuruwan Ikko da Kano da Maiduguri da sauransu, wanda su kuma suke fitarwa zuwa kasashen ketare.
A duk lokacin da kakar aikin ya kama, wanda yake farawa daga watan 10 ko 11 har zuwa watan hudu lokacin da ruwan sama ke fara sauka a yankin, za ka ga kowane layi ka zaga a cikin garin ko ta ina ana aikin citta.Domin yin dubi ga irin alherin da mata da kananan yara ke samu musamman a irin wannan lokaci, Aminiya ta zaga wuraren da dama da ake aikin kusan a ko ina a cikin garin Kafanchan, inda ta tattauna da wasu mata da kuma kananan yara.
Nasir Saddam, yaro ne dan shekara 12 da ke aji biyu na firamare.“Yanzu da ka ganni a nan ina aikin citta saboda ana hutun makaranta ne, amma idan an koma ba zan samu yi ba sai dai sau biyu kawai a karshen mako. Muna tsince tsakuwa ne da yayi da kashin dabbobi da danyen citta sai mu ware tsantsar cittan. Idan mun gama sai masu durawa a cikin buhu su rika durawa shi kuma yayin da muka ware, sai masu shika su zo su saka matankadi da kwandunan roba su rika dagawa suna shekewa har a sake tace citta masu kyau a ciki. A rana ina yin aikin buhu daya zuwa shida, kuma kowane buhu muna yinsa ne kan naira casa’in zuwa Naira dari. Ina samun abin da ya kama daga naira dari biyu zuwa dari biyar a rana,” inji shi.
Ko me Nasir ke yi da kudin idan ya samu? Saiya ce, “Ina samun kudin kashewa kuma ina yin tarin kudin sayen kayan sallah.”

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited