‘Ya dace a kafa manyan kasuwanni a kan iyakokin Najeriya’
Tuesday 27 June 2017     2 Shawwal 1438

Aminiya

A+ A A-

‘Ya dace a kafa manyan kasuwanni a kan iyakokin Najeriya’

Daga Bashir Lawal Zakka, Birnin Kebbi

An yi kira ga gwamnatin tarayya, Najeriya da ta kafa manyan kasuwannin a garuruwan da ke kan iyakokin qasar nan domin habvaka tattalin arzikin da kuma sauran qasashen Afirka da ke da iyaka da Najeriya.
Wani fitaccen xan siyasa a Jihar Kebbi Alhaji Hassan Adamu Lolo shi ne yayi wannan kiran a lokacin da yake zantawa da Aminiya a garin Lolo wanda yake kan iyaka da Jamhuriyar Benin da kuma Jamhuriyar Nijar.
Alhaji Hassan ya ce haka ya biyo bayan alqawarin da gwamnatin Jihar Kebbi tayi nakafa kasuwar duniya da tashar aje kaya da ake shigowa da su daga qasashen qetare da kuma fita da su waje.
Ya ce garin Lolo yana da duk abubuwan da ake buqata na kafa wannan kasuwar duniya da suka shafi shinkafa, kifi da kuma shanu, akwai hanyoyin shigowa da kaya daga waje ta Kogin Kwara da kuma hanyar qasa kowane mako ’yan kasuwa suna zuwa daga qasashen Mali da Sanegal da Nijar da kuma Jamhuriyar Benin.
A qarshe ya ce suna godiya ga Gwamnan Jihar Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu bisa qoqarin da yake yina ganin wannan alqawari ya cika don qara dankon zumunci tsakanin Najeriya da sauran qasashen Afirka.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited