Yadda na samu taimako na fara kasuwanci – Malam Auwal
Tuesday 27 June 2017     2 Shawwal 1438

Aminiya

A+ A A-

Yadda na samu taimako na fara kasuwanci – Malam Auwal

Xan kasuwa Malam Auwal Aliyu MuhammedAminiya ta zanta da wani xan kasuwa Malam Auwal Aliyu Muhammed xan asalin Qaramar hukumar Qunci da ke Jihar Kano wanda ke zauna a garin Xaki-Biyu da ke unguwar Jabi, babbar birnin tarayya Abuja, kuma yake taimakon mutane. Ya shaida wa Aminiya yadda sarkin Unguwar Xaki Biyu ya taimakeshi da wajen da ya fara kasuwanci har zuwa yanzu inda yake ci gaba da zama ina kasuwanci. Ga yadda tattaunawar ta kasance

Aminiya: Za musu ka gabatar da kanka?
Sunana Auwal Aliyu Muhammed, ni xan asalin garin Kano ne, garin Xandaxi, qaramar hukumar Qunci, sannan kuma yanzu ina zaune a nan garin Abuja kuma zuwa yanzu na yi fiye da shekara 15 a garin Abuja ina karatu ina karantarwa, kuma ina kasuwanci.
Aminiya: Waxanne irin kayayyaki kake sayarwa?
Ina sayar da kayyaki ne da suka haxa da lemon kwalba da kuma sayar da shayi da dai sauransu.
Aminiya: Mene ne alaqar da sarki?
Sarki kamar uba ne a wajena, domin ni talakarsa ne, kuma tun da na sauka a Abuja, a garinsa nake zama, kuma akwai alaqa sosai ta mutunci tsakanina da shi, ya xauke ni kamar xansa, hakan ya sa ya ba ni waje domin in fara kasuwanci saboda tausayi ga talakawa, sannan kuma da wasu wurare da ya bayar da nake wakiltar mutanen da ke kasuwanci ko sana’a a wajen, kuma duk da cewa akwai wanda nake wakilta da ya rasu, amma saboda sarki yana da tausayi da adalci, sai ya bar wajen a wajena domin a ci gaba da nema wa iyalan mamacin abinci.
Aminiya: Wane rufin asiri ka samu albarkacin wannan?
Gaskiya sanadiyyar wannan kasuwanci da kuma taimakon sarki, na samu rufin asiri sosai, ina ci ina sha, kuma ina taimaka wa wasu da dama, shi ya sa nake godiya ga sarki sosai domin ta sanadiyyarsa ne na samu damar nan, har kuma ni ma nake taimaka ma wasu.
Aminiya: Mene ne shawaranka ga mutane baqi da ke zuwa Abuja neman abinci?
Shawarata a nan gaskiya ita ce su riqe mutuncinsu, kuma mafi muhimmanci ma shi ne su nema wajen da za su zauna na kirki, sannnan kuma ya kamata mutane su gode wa Allah da abin da ya ba su, domin haka ne kawai zai sa Allah Ya qara musu, sannan kuma ya sa wa abin da suke samu albarka. Sannan kuma su riqe Allah, domin duk wanda ya riqe Allah, to lallai Allah zai taimake shi. Daga qarshe ina addu’ar Allah Ya qara wa sarki lafiya da nisan kwana, kuma Allah Ya qara wa shugaban qasa Muhammadu Burari lafiya kuma ya dawo mana da shi lafiya.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited