Gwamnati ta vullo da tsare-tsare don tallafa wa qananan ’yan kasuwa -Ministar Ciniki
Tuesday 27 June 2017     2 Shawwal 1438

Aminiya

A+ A A-

Gwamnati ta vullo da tsare-tsare don tallafa wa qananan ’yan kasuwa -Ministar Ciniki

Qaramar Ministar Maaikatar Ciniki da Kasuwanci da kuma Masanaantu Hajiya Aisha AbubakarQaramar Ministar Ma’aikatar Ciniki da Kasuwanci da kuma Masana’antu, Hajiya Aisha Abubakar ta ce Gwamnatin Tarayya ta xauki matakan da suka dace don bunqasawa tare da tallafa wa qananan ’yan kasuwa a qasa baki xaya.

Hajiya Aisha Abubakar ta yi furucin ne yayin da take jawabi a wurin taron qarawa juna sani na wuni xaya da bajekolin kayayyakin da mata ’yan kasuwa suka sana’anta wacce qungiyar Matan Afirka ’Yan Kasuwa (AWEP) ta shirya a Abuja a ranar Talata.
Ta ce ‘Tuni wannan gwamnati ta vullo da tsare-tsare don bunqasa kasuwancin mata da qananan ’yan kasuwa kuma Ma’aikatar kasuwanci da ciniki da masana’antu ta qasa ta riga ta fara aiwatar da waxannan tsare-tsare”.
Ta bayyana cewa gwamnatin ta tsoma bankin ciniki da zuba jari na qasa don bunqasa qananan masana’antu tare da bayar da tallafi ga waxanda ke noman tumatir.
Ta qara da cewa tsarin zai baiwa qananan ’yan kasuwa damar samun jari cikin sauqi ba tare da wata matsala ba.
Ta ci gaba da cewa ma’aikatar kula da ingancin kaya ita ma ta xauki matakan ladaftar da masu shigo da kayayyaki marasa inganci tare da raba su a tsakanin jama’a.
Ta bayyana cewa ma’aikatar yi wa kamfanoni rijista ita ma ta rage kuxin da take karva na yi wa kamfanoni da masana’antu rajista da kashi 50.
Ta ce gwamnati ta xauki matakan ne don tabbatar da ganin masu qananan masana’antu da qananan ’yan kasuwa sun samu damar shigar da hajarsu tare da samun riba ba tare da wata matsala ba.
Da take jawabi, Shugaban Qungiyar Matan Afirka ’Yan Kasuwa (AWEP), ta reshen birnin tarayya Abuja, Hajiya Samira Jibir, ta bayyana cewa sun shirya taron ne don su taimaka wa mata su cimma nasara a kasuwancinsu da suka sanya a gaba.
Hajiya Samira ta bayyana cewa babbar matsalar da mata ke fuskanta musamman a birnin tarayya na Abuja shi ne yadda za su samu rancen kuxi da za su bunqasa kasuwancinsu cikin sauqi.
Ta ce membobinsu na Abuja na fuskantar qalubale wajen samun rancen kuxin da za su bunqasa sana’o’insu.
Saboda haka sai ta yi kira ga mambobinsu da su qoqarta su bi qa’idojin da suka dace na yi wa sana’o’insu rajista don cin gajiyar tallafin gwanmati.
Ta yi kira ga gwamnati ta xauki matakan da suka dace don tallafawa mata su riqa samun rancen kuxi cikin sauqi ba tare da fuskantar wata matsala ba.
Ta ce hakan shi zai sa mata su bunqasa sana’o’in tare bunqasa tattalin arziki da kuma samar da ayyukan yi a tsakanin.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited