Mata ’yan kasuwa sun baje-kolin hajojinsu a taron kungiyar AWEP
Tuesday 27 June 2017     2 Shawwal 1438

Aminiya

A+ A A-

Mata ’yan kasuwa sun baje-kolin hajojinsu a taron kungiyar AWEP

Mata ’yan kasuwa daga sassa daban-daban na birnin tarayya Abuja sun gudanar da taron bajekolin kayayyakin da suka sarrafa a karkashin jagorancin kungiyar matan Afirka ’yan kasuwa da ake kira AWEP.
Hakazalika mambobbin kungiyar AWEP sun gudanar da taron karawa juna sani kan dabarun kasuwanci a birnin tarayya Abuja a karshen makon da ya gabata.
Taron wanda kungiyar ta yi masa taken: “Sake gina tattalin arzikin Najeriya ta hanyar damawa da mata,” ya samu halartar mata masu sana’o’in hannu da saye da sayarwa.
Kayayyakin da aka baje a wurin taron sun hada da kayayyakin taba-ka-lashe da kananan masana’antun mata suka sarrafa da kayan abinci da kawa da kayan shafe-shafen mata da makamantansu.
Da take jawabi Ministar Ma’aikatar Kasuwanci da Ciniki da Zuba Jari, Hajiya Aisha Abubakar ta bayyana cewa jigon taron da kungiyar ta zaba ya dace idan aka yi la’akari da halin da mata ke ciki.
Ta bayyana cewa idan mace ta samu ilimi kuma aka tallafa mata to babu shakka tamkar an tallafa wa ci gaba ne da kuma tattalin arzikin kasa.
Ta kara da cewa duk da irin kalubale da ake fuskanta na tattalin arzikin mata na da moriyar da za su ci ta hanyar kasuwanci.
Ta yaba wa kungiyar mata ta AWEP da ta bullo da shirin inda ta ce shirin zai taimaka wa mata ta hanyar bunkasa kasuwancinsu da kuma sana’o’insu.
A jawabinta, shugabar kungiyar AWEP ta kasa, Zainab Jaji ta bayyana cewa shirin na daga cikin dimbin tsare-tsaren da kungiyar ta bullo da su don tallafa wa mata.
Ta bayyana cewa babbar kalubalen da suke fuskanta shi ne na fahimtar da mata muhimmanci rijistar sana’o’insu a ma’aikatar da ke rijistar kamfanoni.
Ta ce yin hakan zai bai wa mata damar samun tallafi daga gwamnati da kungiyoyi daban-daban.
Ita kuwa shugabar kungiyar AWEP ta birnin tarayya Abuja, Hajiya Samira Jibir ta yi kira ga mata su hada kai don cimma burin da kungiyar ta sanya a gaba.
Ta bayyana cewa taron da suka shirya zai bai wa mata damar tallata hajojinsu tare da samun karin kwarewa a fannin kasuwanci.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited