Masu kawo kayan sata ne matsalar kasuwarmu - Shugaban Kasuwar GSM
Tuesday 27 June 2017     2 Shawwal 1438

Aminiya

A+ A A-

Masu kawo kayan sata ne matsalar kasuwarmu - Shugaban Kasuwar GSM

An bayyana shigar bata gari cikin harkokin kasuwancin Kasuwar Hada-hadar Wayar GSM ta Famsanta a matsayin kalubalen da ke kawo tarnaki ga harkokin kasuwaci a kasuwar.
Wannan bayani ya fito daga Shugaban Kasuwar Alhaji Umar danfulani a lokacin da yake tattaunawa da Aminiya a Kano.
Alhaji dan Fulani ya bayyana cewa shugabancin kasuwar yana fuskantar matsala sosai game da yadda irin wadanann bata gari ke kawo musu matsala a kasuwarsu. “Babban kalubalenmu shi ne wadanann bata gari da kullum muke fama da su. Za su je su sato wayoyi su kawo cikin kasuwarmu su sayar, haka za a zo a yi ta rigima. Wani lokacin za a kama su a mika su ga ‘yan sanda inda za a kai su kotu a yi musu hukunci, amma kwana kadan sai su sake dawowa. Ko a kwanan baya wasu bata gari sun kawo wasu wayoyi kasuwar inda har ‘yan sanda suka biyo kayan, bayan bincike ya nuna cewa an kawo kayan kasuwarmu. Haka muka yi ta fama don har sai da muka je har can Kaduna kafin daga bisani abubuwa suka warware. Wannan ba karamin kalubale ba ne a gare mu,” inji shi.
Har ila yau, shugaban ya dora alhakin ci gaba da faruwar wanann lamari a kan ‘yan kasuwar wadanda ke yin kunnen uwar shegu da dokokin kungiyar. “Muna da dokokin kungiya wanda suka bayyana yadda ya kamata ‘yan kasuwa su gudanar da kasuwancinsu musamman bangaren abin da ya shafi sayen wayoyi daga jama’a. Mun ajiye cewa kada mutum ya sayi waya musamman irin masu tsadar nan daga hannun kowane mutum sai ya tabbatar da sanin sa ma’ana ya san wani abu akan sa, ya nemi ya nuna masa wani katin shaidarsa da kuma cikakken adireshinsa, don gudun sayen kayan sata. Duk da cewar mun san maso abin ka ya fi ka dabara, amma mun yi imanin idan ana bin wannan doka za a samu saukin abubuwa da dama. Sai dai akwai masu son zuciya a cikinmu da ke fatali da wanan doka tare da bin son zuciyarsu don tunanin abin da za su samu idan bai taka kara ya karya ba.”
Alhaji danfulani ya kara da cewa shugabancin kasuwa ba ya yin sako-sako wajen zartar da hukunci akan duk wanda suka samu da hannu dumu-dumu cikin sayen kayan sata “muna daukar mataki akan ‘yan kasuwarmu masu son zuciya a yanzu haka mun dakatar da wasu da yawa wadanda muka same su da laifin sayen kayan sata, ma’ana da saninsu, hakan ya sa muka dakatar da su daga kasuwa saboda kin bin doka da suka yi, don kuma ya zama darasi ga na baya. Baya ga haka akwai wasu da muke hukunta su ta hanayoyi daban-daban. Wannan kuma bai bar wani bangare ba indai mutum mamba ne hukunci zai hau kansa ko waye shi,” inji shi.
Sai dai a cewar Alhaji danfulani a yanzu haka shugabancin kasuwa yana ta kokarin daukar wasu manyan matakan don ganin sun dakile ayyukan wadannan bata gari tare da kawar da su daga kasuwarsu.
Hakazalika, shugaban ya yi kira ga ‘yan uwansa ‘yan kasuwa da su ci gaba da ba shugabancin kasuwa cikin hadin kai don a gudu tare a kuma tsira tare. “Ba mu da wurin da ya fi kasuwar nan, nan muke samun abin da muke gudanar da rayuwarmu. Don haka muna kira ga ‘yan uwanmu ’yan kasuwa da su ba mu hadin kai wajen ganin an tsaftace harkokin kasuwanci a cikin kasuwar. Wanann ba zai samu ba sai sun zama masu bin doka da oda da kuma yin kasuwanci bisa hanya ingantacciya bisa koyarwar addini tare da bin dokokin kungiya,”inji shi. Bugu da kari, shugaban ‘yan kasuwar wayar ya yi kira ga gwamnati da jami’an tsaro da su kara tallafa musu. “Babu shaka akwai kyakkyawar fahimta tsakaninmu da gwamnati da kuma jami’an tsaro ta yadda suke ba mu gudummawa a duk lokacin da bukatar hakan ta taso, idan har aka ce wata matsala ta taso sukan ba mu taimako har a samu a warware matsalar cikin ruwan sanyi, sai dai muna neman su kara ribanya taimakonsu kan wanda suka saba yi,” inji shi.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited