Dala ta ci gaba da faduwa a kasuwar bayan fage
Tuesday 27 June 2017     2 Shawwal 1438

Aminiya

A+ A A-

Dala ta ci gaba da faduwa a kasuwar bayan fage

Farashin Dala ya ci gaba da faduwa sosai a karon farko a kasuwannin bayan fage da ke kasar nan, mako guda bayan da babban bankin kasar nan CBN, ya bayyana matakin bunkasa samar da ita ga masu nema a bankuna.
Matsalar karancin Dala a bankunan Najeriya wanda sakamakon rashin wadatar kudaden kasashen wajen a CBN, ya sa Dalar ta yi ta tashin gwauron zabi, a kasuwannin bayan fage na kasar.
Wasu na ganin wannan ne dalilin da ya sa kayayyakiin masarufi da na amfanin yau da kullum suke kara hauhauwa, duba da cewa kasar ba ta faye fitar da kaya zuwa wasu kasashe ba, kamar yadda BBC ta bayyana.
Hakazalika kudaden kasashen wajen da take samu ya ragu sakamakon rage sayen man fetur dinta da Amurka ta yi, da kuma janyewar masu zuba jari.
Malam Sani ya ce hakan ba zai rasa nasaba da sanarwa da gwamnati ta yi ba na cewa CBN za ta kara yawan Dalar da take bai wa bankuna.
“Kuma ka ga ba a bata lokaci ba wajen fara ba su, don a ranar Alhamis din makon jiya ma naje banki kuma na ga wani ya karba, matafiyi ne kuma an sayar masa da ita a kan naira 375 duk Dala guda, bayan kuwa da safe ana sayar da ita a nan kasuwa 505,” inji shi.
Ya kara da cewa, “Amma yanzu kuma maganar da nake da yamman nan (ranar Talata), ganin bankuna suna bayarwa, yanzu a kasuwa ta dawo 455 zuwa 460.”
Wasu rahotannin ma sun ce a makonni biyu da suka gabata sai da aka sayar da duk Dala daya a kan Naira 516. ‘Yan kasuwar sun ce in abin ya dore, to farashin zai iya dawowa daidai a bankuna da kasuwar bayan fage.
‘Yan kasuwar dai sun ce fatansu shi ne Dalar ta yi ta sauka domin a samu saukin rayuwa.
Masana tattalin arziki sun ce abin bai zo da mamaki ba, kuma idan har matakin bankin ya dore to lallai za a samu sauki sosai.
A ranar Litinin din makon jiya ne CBN ya sanar da cewa ya fitar da wadansu sababbin manufofin musayar kudaden waje.
A karkashin sabon tsarin, Babban Bankin ya ce zai kara yawan kudaden wajen da ya ke bai wa bankunan kasar da nufin saukakawa ‘yan Najeriya masu bukatar zuwa asibiti a wasu kasashen, da masu karatu a wasu kasashen da kuma ‘yan kasuwa.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited