‘Za a iya amfani da yawan matasan kasa don bunkasa tattalin arziki’
Monday 26 June 2017     1 Shawwal 1438

Aminiya

A+ A A-

‘Za a iya amfani da yawan matasan kasa don bunkasa tattalin arziki’

Manajan Daraktan Bankin Masana’antu (BOI), Mista Waheed Olagunju ya ce yawan matasan kasar nan wata kadara ce da za a iya amfani da ita wajen bunkasa tattalin arziki tare da shawo kan dimbin kalubalen  da ake fuskanta.
Ya yi jawabin ne a lokacin da yake kaddamar da shirin tallafa wa matasa na ‘Youth ignite project,’ a Legas, wanda shirin hadin gwiwa ne tsakanin bankinsa da Bankin First da aka tsara don samar wa matasa miliyan guda abin dogaro da kai kowace shekara.
Ya ce bankins ane jigo wajen aiwatar da shirin, saboda akwai tabbacin cewa bai wa dimbin matasa abin yi zai yi tasiri wwajen shawo kan matsalar tattalin arzikin kasa da ake fama da ita a kasar nan.
Ita kuwa shugabar Hukumar Gudanarwar Bankin First, Misis Ibukun Awosika, ta jajirce wajen tabbatar da bukatar ganin matasa sun samu abin yi ta yadda za su bayar da gudunmuwarsu wajen tallafa wa bunkasar tattalin arzikin kasar nan.
Ta ce dole ne matasa su baje kolin basirasu tare da aikin da iliminsu ta yadda za su aiwatar da managartan tsare-tsare a cikin kasar nan.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited