Ana amfani da kananan bankuna wajen cin rashawa - Ministar kudi
Monday 26 June 2017     1 Shawwal 1438

Aminiya

A+ A A-

Ana amfani da kananan bankuna wajen cin rashawa - Ministar kudi

Gwamnatin Tarayya ta gano yadda masu zamaba cikin aminci da wasu ma’aikatan gwamnati ke amfani da kananan bankuna wajen satar kudi a kasar nan, kamar yadda yake kunshe a wasikar Ministar Kudi Misis Kemi Adeosun zuwa ga Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Mista Godwin Emefele.
A wasikar da minister ta aike wa Gwmanan Babban bankin, ta bukaci hadin kansa wajen fadada lambar tantance masu ajiya a bankuna zuwa ga kananan  bankunan, ta yadda za a tantance masu ajiya a cikinsu; kuma ko a gano asusun ajiyar ma’aikatan bogi da batagari ka iya budewa su rika kwasar kudi.
Ta ce bullo da lambar tantance masu ajiya a bankuna ta BbN da Babban bankin (CBN) ya yi, ta taimaka matuka gaya wajen tabbatar da nagartar tsarin biyan albashi na gwamnatin Tarayya, al’amarin da ya bayar da damar gnao ma’aikatan bogi har dubu 50, wadanda aka tsame su.
A wata takardar da ta fito daga Ma’aikatar Kudin dauke da sa hannun Daraktan Yada Labarai, Salisu  Na’inna dambatta, Misis Adeosun ta ce bude asusun ajiya a kananan bankuna ba tare da lambar tantance masu ajiya ba, ya bude babbar kafa da miyagu ka iya amfani da ita wajen aikata mummunar hada-hadar kudi, tare da boye kudin sata wadanda ba lallai ne a gano su ba.
Misis Adeosun ta yi wa Gwamnan Babban Bankin (CBN) nuni da cewa, kafin a kayyade lokacin samun lambar tantance ajiyar asusun banki, an samu dimbin ma’aikatan gwamnatin tarayya, wadanda suka sauya asusun ajiyarsu daga bankunan kasuwanci zuwa kananan bankuna, kamar yadda aka lura.
“Wannan abin da ake zargi da mummunan aiki, tuni aka fara bin kadinsu, ta yadda za a gano zamba cikin aminci,” kamar yadda ministar ta bayyana.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited