Bashi na iya tursasa wa Etisalat ficewa daga Najeriya - Rahoto
Monday 26 June 2017     1 Shawwal 1438

Aminiya

A+ A A-

Bashi na iya tursasa wa Etisalat ficewa daga Najeriya - Rahoto

Kamfanin sadarwar wayar salular Abu Dhabi na Etisalat bashi na iya tursasa masa sayar da hajarsa a Najeriya, inda bashin ya kai Dala biliyan da miliyan 200, amma ana son kamfanin ya wkartware badakalar kafin daukar matakin, kamar yadda wasu majiyoyi biyu suka bayyana wa Kamfanin Reuters a ranar Litinin din da ta gabata.
Babban bankin Najeriya da hukumar daidaita harkokin sadarwa  sun yanke matsaya, inda suka yi yarjejeniya da bankunan kan sun bi hanyoyin warware badakalar bashi, maimakon kwace kamfanin Etisalat don gudun kawo cikas ga masu zuba jari, ta yadda za a samu damar kauce wa karuwar bashin.
Etisalat dai ya shirya ganawa da masu bashi a ranakun talata da Laraba da suka gabata.
Har yanzu dai ba a yanke matsaya ba kan ko Etisalat da ke da kashi 45 cikin 100 nja hannun jarin Najeriya bhayan an warware badakalar bashin cikin Fabrairu, ta yadda za su zare hannunsu gaba daya.
Aminiya ta gano cewa tattaunawar bankunan da kamfanin wayar salular an yi ta ne kan yadda za a biya bashin.
Wata majiya daga gwamnati ta bayyana cewa Etisalat ya nemi a kara masa lokaci don biyan bashin, bukatar da ake sa ran bankunan za su amince d aita, kamar yadda  majiyar ta bayyana.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited