Sakonnin masu karatu – tes da imel (7)
Friday 28 July 2017     4 Zulki'da 1438

Aminiya

A+ A A-

Sakonnin masu karatu – tes da imel (7)

Assalamun alaikum, da fatan kana lafiya a masu karantun mu wannan mako ma ga mu dauke da ci gaban amsoshin sakonninku ta Imel.  Sakonnin da suka rage yanzu na wayar salula ne.  Nan da makonni uku masu zuwa zan zubo su, daga nan kuma za mu shiga sabon babi cikin fagen kere-kere in Allah ya yarda.

Assalamu Alaikum Baban Sadik don Allah ka yi min karin bayani a kan yadda ake kirkirar maudu’i a shafin twitter wato “hashtag#”, kuma ta yaya mutum zai iya gane wanda ya kirkiri maudu’in? Sannan ta yaya ake tantance shafukan sada zumanta irin su Facebook da Twitter, wato berified? Nagode. Daga Bello Isiyaku: This email address is being protected from spambots. You need JavaScript enabled to view it.
Wa alaikumus salam. Malam Bello, barka dai. kirkirar hashtag ba wani abu bane mai wahala. Idan kana da wani sako dake dauke da wata manufa da kake son yadawa nan take a Twitter misali, sai ka rubuta sakon, sannan ka tsara kalmomi ko haruffan da kake son su wakilci wannan sako, ko dai a farkon sakon, ko kuma a karshen sakon. Ga misali: “Wajibi ne kowa ya dage wajen tarbiyyar ‘ya’yansa. Ba mu yarda da sakakkiyar ‘yanci ga yara da nufin gata ba. #TarbiyyaWajibi”. Ka ga sakon da na rubuta mai dauke da manufata, kan tarbiyya ne, da nuna inkari ga masu bai wa ‘ya’yansu sakakkiyar ‘yanci a rayuwarsu da sunan gata. Amma a dunkule, ina nuna dole ne iyaye su kula da tarbiyyar ‘ya’yansu. Shi ya sa na sanya taken hashtag dina: #TarbiyyaWajibi.
Kana iya rubuta sakon da kowane harshe cikin harsunan duniya da ka nakalta. Amma dole ne ya zama wadanda kake son su fahimci sakon suna jin harshen. Da zarar ka rubuta ka aika, duk wadanda suke abota da kai za su gani. Da zarar su ma sun dauki sakon (“retweet,” kamar “share” ke nan a Facebook), zai kai ga abokansu, su ma daga can idan suka dauka, haka abin zai ta yaduwa.
Dangane da tambayarka ta biyu kuma, gane asalin wanda ya kulla hashtag abu ne mai wahala ainun. Domin masu dandalin Tweeter ba su samar da wani tsari na musamman da za a iya amfani da shi, ta hanyar tambaya (Search) ko nemo wanda ya assasa hashtag din ba, a farkon lamari. Sai dai nan gaba in shafin bai rufe ba, ta yiwu cikin tsare-tsaren da suke samarwa lokaci zuwa lokaci, za su tsara wata hanya don yin hakan.
Tambayarka ta karshe kan batun tantance shafin mai shafi a Facebook, wato: “berified Pages,” tsari ne da masu shafin Facebook ke aiwatar da shi, don nuna ingancin shafin da mai shafin. Ma’ana, idan ka shiga shafin wani gwarzo ko wani kamfanin kasuwanci a Facebook, ka ci karo da wata alama shudiya da maki fari a kanta, wannan na nuna cewa wannan shafi ne ingantacce, ba na bogi ba. Sun samar da wannan tsari don tabbatar da natsuwa a zukatan masu son aiwatar da saye da sayarwa a dandalin Facebook ta hanyar shafukan kasuwanci da ke da rajista a dandalin. Ganin cewa shafukan bogi sun yawaita sosai, idan ba haka suka yi ba, to, kamfanonin da ke ba su tallace-tallace za su ragu, ko ma a rasa gaba daya. Domin jama’a ba za su amintu da abin da suke tallatawa ba, tunda babu tabbacin ingancin shafin.
Samun hukumar Facebook su tantance shafinka a matsayin shafi ingantacce (berified Page) abu ne mai sauki. Sai dai ba kowace nahiya daga cikin nahiyoyin duniya suka tanada wa wannan tsari ba. Mu a nan Afirka ba mu cikin wadanda za su iya neman hukumar Facebook su tantance mana shafukanmu. Don haka ma ko ka je shafin da ake aika wannan bukata ba za ka ga alamar da za ka yi amfani da ita wajen aika bukatarka ba. Sun yi haka ne ganin cewa kamfanoni da shahararrun mutanen da ke da shafuka da su galibi suna kasashe mawadata ne. Da fatan ka gamsu.
Assalamu alaikum, don Allah ina son a fahimtar da ni kan tauraron dan Adam; wane aiki yake yi a sararin samaniya? Shin, akwai mutane a cikinsa ne? Daga Abdoul Madjidou daga Libya: This email address is being protected from spambots. You need JavaScript enabled to view it.
Wa alaikumus salam Malam Abdul Madjidou, da fatan kana cikin koshin lafiya. Wannan tambaya ce mai matukar mahimmanci, kuma tana cikin tambayoyin da suke yawan maimaituwa a wannan shafi mai albarka. Don na kebance wannan lokaci don fadada bayani iya gwargwado.
Da farko dai, Tauraron dan Adam shi ne duk wata na’ura mai cin gashin kanta da ake harbawa zuwa sararin samaniya don mika wa da karbo bayanan yanayi ko dauko hotunan wasu wurare da dan Adam ba ya iya kaiwa garesu ta dadi, ko kuma sunsuno irin yanayin da mahalli zai kasance a wasu lokuta na daban, ko kuma don yada bayanan sadarwa daga wani bigire na duniya zuwa wani bigire. Ire-iren wadannan taurari suna shawagi ne a cikin falakin wannan duniya tamu, ko duniyar wata da taurarin da Allah Ya halitta, ko kuma cikin falakin wasu duniyoyi makamantan namu. A halin wannan shawagi ne suke gudanar da ayyukansu na nemo bayanai, ko karbowa daga wani bangaren wannan duniya don yada bayanan zuwa wasu bangarorin daban, ko kuma nemo bayanan da ke da nasaba da falakin da suke shawagi a ciki, don aiko sakon da suka taskance zuwa garemu a wannan duniya, ko kuma, a wasu lokutan, su dauko mana hotunan abin da ke faruwa ga manya-manyan tekunan da ke zagaye da mu a duniya gaba daya.
An fara harba ire-iren wadannan taurarin wucin-gadi ne zuwa cikin falaki shekaru kusan 50 da tara da suka gabata (1957), kuma ya zuwa yanzu, an harba wajen dubai masu zuwa don karbowa da aikawa da bayanai ko sunsuno yanayi ko kuma dauko hotunan sararin samaniya, don amfanin dan Adam. A karon farko ana amfani ne da roket ne mai dauke da kumbo (space shuttle), don cilla wani tauraro zuwa sararin samaniya. Daga baya aka zo ana amfani da jiragen sama masu masifar gudu, duk da yake shi ma wannan tsari na bukatar roket wanda ke harba jirgin zuwa wani mizanin nisa cikin samaniya, kafin wannan jirgi ya ingiza tauraron cikin falaki.
Ana cikin haka sai kuma masana kimiyyar sararin samaniyar Amurka suka bullo da wata hanya, wacce ta sha bamban da sauran wajen sauki da inganci. Wannan hanya kuwa ita ta cilla tauraron dan Adam daga babbar kumbon tashar binciken sararin samaniya da ke can sararin samaniya, wato US Space Shuttle. Hakan na faruwa ne domin masana na iya kera tauraron dan Adam a halin zamansu cikin wannan kumbo da ke tashar, har su harba shi. Haka idan ya lalace ko ya gama aikinsa, suna iya sanya shi cikin wani kumbo karami don aikowa da shi wannan duniya tamu don a gyara shi yadda ya kamata. Nan gaba, masana harkar falaki a Amurka na tunanin bullo da wani tsari mai suna Single Stage to Orbit, wato “tsalle daya zuwa falaki”, a misali. Wannan tsari zai rage yawan tashoshin da tauraron dan Adam zai bi kafin kaiwa ga falakin da aka tunkuda shi don gudanar da aikinsa. Idan har suka dace, wannan tsari zai zo ne da kumbon sararin samaniya guda daya, tafkeke, mai iya daukar taurarin dan Adam da dama, don aikawa da su zuwa cikin falakin da ya dace da su, cikin harbawa guda!
Tauraron dan Adam na farko da ya fara shiga cikin falakin wannan duniya tamu shi ne Sputnik 1, wanda kasar Rasha ta harba a ranar 4 ga watan Oktoba, shekarar 1957. Wannan tauraro ya yi shawagi cikin falaki yana aiko sakonni har tsawon kwanaki 21. Bayan ya kamo hanyarsa ta dawowa duniya, sai ya kone a hanya. Hakan ya faru ne ranar 4 ga watan Janairun shekarar 1958. Daga nan kasar ta sake cilla wani tauraron mai suna Sputnik 2, a ranar 3 ga watan Nuwanba na shekarar 1957 dai har wayau. A ciki suka sanya wata karya don gwaji, wacce a karshe ta mace, sa’o’i biyu da harba ta, sanadiyyar tsananin zafin da ke cikin tauraron da aka sanya ta ciki. Tauraron Sputnik 2 ya dawo wannan duniya tamu ranar 14 ga watan Afrailun shekarar 1958, inda ya kone bayan ya shigo shi ma.
Da ganin haka sai kasar Amurka ta fara narkewa da kishi. Nan take sai kawai aka ji ita ma ta harba tauraronta na farko zuwa cikin falakin wannan duniya tamu, mai suna Edplorer 1, ranar 31 ga watan Janairun shekarar 1958. Bayan nan ta sake cilla wani tauraro mai suna Discoberer 13, tauraron dan Adam na farko da ya fara zuwa falaki, ya taskance bayanan da yake bukata ta hanyar wata na’ura, sannan ya cillo wannan na’ura zuwa wannan duniya tamu, masu binciken kasar Amurka suka dauka don tantance sakonnin da ya kalato musu. Wannan aiki ta gudanar da shi ne cikin shekarar 1960, ranar 10 ga watan Agusta. Daga nan sauran kasashe suka biyo baya.
Akwai nau’ukan tauraron dan Adam da dama a cikin falaki, masu shawagi don gudanar da ayyukan da aka aike su gudanarwa. A halin yanzu ga bayanan nan filla-filla kan dukkan nau’ukan da ake da su:

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited