Kimiyyar lantarki a sawwaqe (2)
Monday 26 June 2017     1 Shawwal 1438

Aminiya

A+ A A-

Kimiyyar lantarki a sawwaqe (2)

Asali da Samuwa a Taqaice

Wutar lantarki ko makamashin lantarki na daga cikin nau’ukan makamashi da Allah ya samar don moriyar xan adam a wannan duniya. Kamar yadda na tabbata mai karatu yaji wa’azi daga malaman addini, cewa Allah bai halicci wata halitta ba face sai da ya tanada mata arzikinta kafin lokacin halittarta. Daga cikin wannan arziki akwai samuwar duk wani abin da zai taimaka wa xanadam yin rayuwa mai inganci a wannan duniya. Duk wannan gata Allah ya masa ne, don danadam ya samu natsuwa har ya bauta wa Allah hankalinsa a kwance.
Daga cikin makamashin da Allah ya tanada wa xanadam a wannan duniya, gabanin bayyanar ilimin kimiyya ko masana kimiyya su gano irin na zamanin yau. Daga cikinsu akwai sinadaran lantarki da ke samuwa daga walkiya (hasken da ke bayyana kafin samuwar cida) da ke xarsuwa a sararin samaniya. Akwai kuma sinadarai na musamman da Allah ya samar a mahallin duniyar nan da muke rayuwa. Waxannan sinadarai na madda (Atoms) su ne suke haxuwa da juna a bisa qaddara da tsari da kintsin Ubangiji, don samar da caji ko wutar lantarki a mahallinmu. Sinadaran ku wasu ne: “Protons,” da “Neutrons,” da kuma “Electrons.” Haxakar waxannan sinadarai ne ke samar da makamashi ko wutar lantarki. A zamanin da al’ummomi kan haxa abubuwa daban-daban don samar da wannan nau’in makamashi.
Bayan waxannan har wa yau, tarihi ya nuna cewa al’ummomin da suka gabata musamman na qasar Masar da daular Girka na cikin waxanda suka fara gano samuwar makamashin lantarki daga jikin wasu daga cikin dabbobin da ke cikin ruwa, musamman kifaye. Akwai nau’in kifi da ake kira: “Electric Fish,” wanda ke xauke da sinadaran lantarki a jikinsa. Irin wannan kifi idan ka tavashi nan take zai ja ka, kamar yadda wutar lantarki ke jan wanda ya tavashi ba tare da wani shamaki ba. Irin wannan nau’I na kifi shi ake kira: “Electrogenic Fish.” A daya vangaren kuma akwai waxanda su basa xauke da wannan caji na lantarki a jikinsu, sai dai kuma duk inda akwai cajin lantarki ko sinadaran lantarki, suna iya fahimtarsa. Waxannan su ake kira: “Electro-receptive Fish.” Masana kimiyyar lantarki su kace ire-iren kifayen da ke xauke da sinadaran lantarki suna da yawa, sannan an qiyasta qarfin cajin lantarkin da ke jikinsu na tsakanin 60 zuwa 600 ne a ma’aunin lantarki na “Volts” (60 - 600volts).
Bayan dabbobin ruwa da sinadaran mahalli da ke haddasa samuwar makamashin lantarki, jikin xanadam ma yana xauke da sinadaran lantarki. Wannan vangare kuwa shi ne kwakwalwarsa. Idan mai karatu bai mance ba, a doguwar qasidarmu mai take: “AsalinTunani: Tsakanin Kwakwalwa da Zuciya,” mun nuna cewa kwakwalwar xanadam na xauke ne da nau’ukan jijiyoyi daban-daban. Daga cikinsu akwai jijiyoyin da ke xauke da sinadaran lantarki masu suna: “Neurons.” Waxannan jijiyoyi masu xauke da tubalin halitta (Neural Cells), su ne ke aikin sadar da bayanai tsakanin vangarorin kwakwalwar xanadam da sauran sassannin jikinsa. Malaman kimiyyar kwakwalwa na wannan zamani sun tabbatar da cewa akwai ire-iren waxannan jijiyoyi masu xauke da sinadaran lantarki sama da biliyan xari (100,000,000,000) a jikinko wane xanadam mai rai.
A wannan zamani kuma da muke rayuwa, fannin lantarkin da mukea mfana dashi ya samo asali ne daga gaggan masana guda uku. Waxannan masana kuwa su ne: Benjamin Franklin, xaya daga cikin masana fannin kimiyya a qasar Amurka, wanda ya fara kwatanta cewa: walqiya da ke samuwa daga sararin samaniya ya yin da ake ciba, yana xauke ne da sinadaran lantarki. Ya gudanar da bincike na musamman a kan haka, don tabbatar da ikirarinsa. Sai kuma Thomas Edison, wanda aka fi danganta wannan fanni gareshi, shi ne babban sanadi wajen samar da kwan lantarki, don janyo makamashin lantarki da amfana dashi a gidaje. Sai mutum na uku, wanda ya samar da tsarin samar da makamashin lantarki da yaxashi ko rarrabashi. Wannan masani kuwa shine Nikola Tesla. Ya rayu ne a karni na 19. Bayan waxannan mutane, akwai xaruruwan jama’a da suka yi ruwa su ka yi tsaki wajen ganin fannin ya havvaka kamar yadda yake a halin yanzu. Cikin dacewar Ubangiji, za mu riqa kawo sunayensu da abin da su ka yi, lokaci zuwa lokaci, idan buqata ta kama.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited