Kimiyyar lantarki a saukake (3)
Monday 26 June 2017     1 Shawwal 1438

Aminiya

A+ A A-

Kimiyyar lantarki a saukake (3)

Tasirin lantarki ga rayuwar  yau
Abu ne sananne cewa rayuwar yau sai da makamashi ko wutar lantarki.  Idan ka kebance kasashe masu tasowa ko k asashe matalauta,  a sauran kasashen Turai da Amurka, kusan duk kauyuka akwai wutar lantarki, ba ma ta birane ake ba.  Wutar lantarki ba wani kayan gabas ba ne a wajensu.  Amma duk da haka, a kasashenmu ma kusan duk rayuwar jama’a ta ta’allaka ne da wutar lantarki.  Tabbas akwai kauyuka da ko da wutar lantarki ko babu za su iya rayuwa yadda suka saba, amma a galibin biranen mu wutar lantarki dole ce.  Meye dalili?  Duk da cewa ba duk sa’o’in yini ake samun wutar lantarki ba, da yawa cikin jama’a sun tanadi na’urar samar da wutar lantarki, wato: janareta ke nan.  Idan ba ka girki da na’urar dumama abinci mai aiki da makamashin lantarki, kana bukatar jin labarai ta hanyar rediyo ko talabijin ko jaridu.  Dukkan wadannan kafofi suna bukatar wutar lantarki don gudanarwa.  
Kamfanin jarida na bukatar kwamfutoci, da na’urar dab’i (Printer), da na’urar sawwara bayanai (Photocopier ko Scanner), da wutar kwayeyen da za su haskaka ginin da ma’aikatan ke aiki, da na’urar sanyaya ofishi.  Dukkan wadannan, su kuma, suna bukatar wutar lantarki don gudanar da ayyukansu.  Idan an gama kintsa shafukan jaridar gabadaya, sai an tura wa babbar na’urar da za ta dabba’asu a matsayin jarida, wanda ita ma tana bukatar wutar  lantarki don gudanuwa.
Idan ka koma bangaren kafar talabijin ma haka lamarin yake, ko ma fiye.  Daga sa’adda aka fara  daukan shiri  har zuwa lokacin gabatar da shi, komai na bukatar wutar lantarki.  A bangaren rediyo ma haka abin yake.  Ba ma wadannan kadai ba, na’urar talabijin da rediyon da za  ka kunna su kansu suna bukatar wutar lantarki; ko dai ta hanyar babbar kafar samar da wutar ko ta hanyar janareta ko batiri.
Idan muka  koma bangaren samar da lafiya, kuma wannan sai dai a yi shiru.  Babu asibitin da zai iya rayuwa a yau, a Najeriya, sai da wutar lantarki.  Tabbas akwai labaran da ke nuna cewa wasu asibitocin kan gudanar da tiyata ta amfani da fitila!  Wannan hadari ne mai girman gaske, idan ma da gaske hakan na faruwa.  Amma duk da hakan ma, ita kanta fitilar, musamman idan wacce ke taskance makamashi ce (Rechargeable), dole tana bukatar wutar lantarki.  Idan ka koma wajen masu gwajin jini a dakunan bincike a asibiti (Laboratory), dole sai da wutarlantaki.  Tabbas akwai nau’ukan gwajin da za ka iya yi (na Maleriya) ba tare da wutar lantarkiba.  Sai dai wannan kadan ne cikin kadan.  Kuma galibin masana na ganin ire-iren wadannan gwaje-gwaje ba lallai ba ne a samu natija cikakkiya ko madogara mai inganci.  
dakunan ajiye gawawwaki sai da wutar lantarki.  dakunan ajiye marasa lafiyar da ke cikin halin-ni-‘yasu (Intensibe Care Unit), sai da wutar lantarki.  Sannan, a karshe, ginin asibitin gabadayansa yana bukatar haske don gudanar da aiki cikin lumana da tsari.  Wannan haske bai samuwa ta dadi sai da wutar lantarki.
Mu koma bangaren  siyasa da shugabanci.  Ofisoshin hukuma dole sai da wutar lantarki.  Eh, kana iya cewa ai a ofishin karamar hukumar ku babu wutar lantarki.  Wannan na wucin gadi ne.  Amma in da za a bi ka’ida kowa ya zo aiki kamar yadda doka ta tanada; daga karamin ma’aikaci zuwa babba, duk a taru a lokaci guda, dole sai an tanadi wutar lantarki.  Domin aiki ba zai yiwu ta dadi ba.  Balle mu koma bangaren ma’aikatun jiha ko na tarayya.  
Wutar lantarki a wadannan wurare jazamun ne!  in ba ka yarda ba, ka taba tunanin a ce ba wuta a billa, gidan shugaban kasar Najeriya?  Ka taba tunanin ba wuta a gidan ko ofishin Gwamnan jiharku?  Ko ka taba tunanin rashin wutar lantarki a ginin majalisun jihohi da na tarayya?  Idan ba ka taba yi ba watakila saboda rashin yadda wuraren suke, billa gida ne kuma ofishi ne na shugaban kasar Najeriya.  Dole sai da wutar lantarki.  “Gobernment House”, kamar yadda ake kira a jihohi, gida ne (ga wasu gwamnonin) kuma ofishi ne ga Gwamnan jihar.  Dole sai da wutar lantaki.  Ginin majalisu na jihohi ma nan ne ake taruwa don tattaunawa kan dokokin da za a yi wa ‘yan jihar.  A bangaren majalisar tarayya kuma da ke Abuja, gini ne na ofisoshin (don akwai ofisoshi sama da 100) ‘yan majalisun tarayya da ke tattauna hanyoyin samar da dokoki ga ‘yan Najeriya.  Zama a wuri irin wannan sai da wutar lantarki.
Mu dawo kan daidaikun ‘yan Najeriya; wayoyin salularmu sai da caji.  Cajin nan bai samuwa sai ta amfani da wutar lantarki.  Da yawa cikinmu mun gwamnace a ce wayoyinmu akwai caji, ko da babu wuta a gidajenmu.  Za mu iya kwana cikin duhu. Ba wannan kadai ba, motarmu ma sai da wutarlantarki.  Sosai kuwa!  In ba ka gane ba, cire wayar da ke saman batirin motarka gwada tayar da ita  ka ga ni ko za ta tashi.  Shiru za ka ji, wai almajiri ya ci shirwa.  
To, kaddara cewa motocin da ke shawagi a kan titunan kasar nan batiransu sun shanye a lokaci guda!  Ya salaam! Me zai faru?  Komai zai tsaya cak.  Saboda batirin mota na dauke ne da sinadaran lantarki.  Shi kan shi batirin yana bukatar caji, shi ya sa ma Bature ya yi masa abin da ke cajashi a yayin da motar ke tafiya ko take kunne.  Wannan na’ura kuwa itace na’ura mai suna: “Alternator” da ke cikin injin motar.  Da zarar babu wannan na’ura, batirin motarka zai shanye, duk tsawon zamani.  Idan kuwa ya shanye, to, babu abin da zai cajashi.  Ka ga kuwa ashe dole sai da wutar lantarki.
A galibin birane kanana da manya a wannan kasa tamu, ana gina rijiyoyi nazamani da ake amfani da su a gidaje.  Wadannan rijiyoyi suna dauke ne da na’urar da ke janyo zuwa cikin rumbun da ke taskanceta.  Wannan na’ura tana bukatar wutar lantarki da zai motsa ta don aiwatar da wannan aiki.  Idan ka koma bangaren manomanmu na karkara musamman masu noman rani, haka lamarin yake.  Na’urar janareta ce ke janyo musu ruwa daga  gulbi ko kududdufi ko korama ko kogi, don shayar da shuke-shuke.  Wannan na’ura ita ma dole tana bukatar wutar lantarki.  Ta ko’ina ka duba haka lamarin yake.
Daga bayanan da suka gabata, mai karatu zai fahimci cewa lallai rayuwa a yanzu dole sai da wannan makamashin wutar lantarki.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited