Kimiyyar lantarki a saukake (4)
Monday 26 June 2017     1 Shawwal 1438

Aminiya

A+ A A-

Kimiyyar lantarki a saukake (4)

Sanayya kan Lantarki

A baya na yi mana mukaddima ne kan mahangar da darasinmu zai dauka kan wannan maudu’i.  Na yi bayanin kadan daga cikin tarihin wannan fanni a takaicen-takaitawa, da bangarorin da za mu dauka.  A wannan karo in Allah Ya so za mu kutsa cikin dakin karatu don bayanin ma’ana da sinadaran da suke haduwa don samar da haske ko makamashin lantarki.  Mai karatu zai ji bayanin wani iri, saboda kalmomin da zan yi amfani da su ba kalmomi ne da aka saba ji ba; ni ne na kirkkresu, don kokarin sawwake fahimtar sakon da nake son isarwa.  
Ma’anar “Lantarki”
Kalmar “Lantarki,” a yadda muke amfani ko furuta ta a harshen Hausa, kalma ce da ta samo asali daga harshen turanci, wato: “Electricity,” wacce ita kuma ta samo asali ne daga kalmar “Electron,” wato asalin sinadarin madda da Allah Ya hore a mahalli ko sahar wannan duniya, don amfanin dan adam.  Malaman kimiyyar lantarki sun hadu kan cewa bayar da ma’anar wannan kalma a ilmance abu ne mai wahala, saboda gamewa da sarkakiyar dake cikin kalmar wajen ma’ana da abubuwan da ta kunsa.  Ma’anar da ake baiwa kalmar kawai ita ce: “fanni ne da ke lura da gudanuwar makamashin lantarki daga mabubbugarsa zuwa inda ake son amfani da shi.”
Misali, idan ka jawo wutar lantarki zuwa cikin gidanka daga magudanarsa (na’urar Transformer ko asalin magudana inda ake samar da ita), sannan ka jona kwamfuta ko talabijin ko akwatin rediyonka ta amfani da waya ta musamman, sannan ka kunna don amfanuwa da na’urar, ka aiwatar da tsarin lantarki kenan.  Wannan ke nuna cewa ma’anar kalmar “Lantarki” na damfare ne da samar da shi; daga magudana zuwa inda za a yi amfani da shi.  Wannan a bisa tsarin samarwa da sarrafa makamashin lantarki na zamani kenan, ba wanda ke samuwa a mahalli kai tsaye ba.
Sinadaran Lantarki da dabi’unsu
Sinadarai ko makamashin lantarki, kamar yadda bayani ya gabata a baya, su ne abubuwan da ke haduwa da juna wajen samar da wutar lantarki.  Allah Ya samar da wasu maddodi (Atoms) na kimiyya a mahallin da muke rayuwa.  Wadannan maddodi na dauke ne da wasu madda nau’uka daban-daban, masu sunaye da dabi’u daban-daban.  Daga cikin wadannan nau’ukan sinadarai akwai guda uku, wadanda su ne ke da alhakin samar da, ko haddasa samuwar makamashin lantarki a mahalli.  Kashi na farko ana kiransu: “Electrons,” wadanda daga sunansu ne aka samu sunan wannan fanni da muke zance a kai.   Kashi na biyu ana kiransu da suna: “Protons.”  Sai kashi na uku da ake kira: “Neutrons.”  
Kamar yadda bayani ya gabata, wadannan sinadarai ko maddodi na kimiyya kowannensu yana da dabi’a.  wadannan dabi’u su ake kira: “Atomic Properties” a harshen fannin lantarki.   Daga cikin dabi’ar lantarki akwai “caji”, ma’ana karfin tasirinsa kenan a inda aka same shi.  Wannan shi ake kira: “Charge” a harshen turancin lantarki na zamani.  Wannan dabi’a ta caji ana iya kiyasta ta, da kuma kididdige karfinta.  Wannan ne ma ya sa kowace irin na’urar lantarki take da iya kimar makamashin lantarkin da za a iya jona mata.  Idan ka sayi talabijin ko akwatin rediyo, ko kwamfuta, akwai iya kimar wutar da za ta iya dauka an rubuta a jikinta.  Da zarar ka bude kundin da ta zo da shi (Manual), za ka gansa a rubuce cikin jerin siffofin da dabi’un na’urar.  An maka haka ne don kada ka jona mata wutar da ta fi karfinta ta kone.  Idan haka ya faru, ba ruwansu; ba za su biyaka ba, domin babu garanti (Warranty) a wannan yanayin.
Caji, wanda shi ne dabi’ar lantarki, ya kasu kashi biyu; akwai caji mai kari, wato: “Positibe Charge” kenan, sannan akwai caji mai ragi, ko ka ce: “Negatibe Charge” kenan.  Akwai nau’i na uku, wanda ba a cika sanya shi cikin lissafi ba, amma yana nan.  Shi ne hakikanin wanda ke kulla zumuncin da ke samar da makamashin lantarki a tsakanin maddodin da bayaninsu ya gabata.  Wannan nau’i na uku na kira shi: “Holoko.”  Aikinsa shi ne daidai nau’ukan caji biyu (kari da ragi), don samar da abin da za a yi amfani d ashi na makamashi.  Kuma shi ne ake kira: “Neutral” a harshen turanci.
Shi wannan sinadari na caji shi ne asali ko madarar makamashin lantarki.  Yana karuwa kuma yana raguwa.  Ya danganci yanayi ko mahallin da ake samar da shi.  Ana iya rarraba shi.  Ana iya takaita shi.  Ana iya kambama shi.  Ana iya sarrafa shi.  Sannan ana iya taskance shi, don amfani da shi a wani lokaci na daban.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited