Amsoshin tambayoyi game da ciwon suga da ciye-ciyen abinci
Saturday 24 June 2017     29 Ramadan 1438

Aminiya

A+ A A-

Amsoshin tambayoyi game da ciwon suga da ciye-ciyen abinci

A game da ciwon suga; idan iyayen mutum suka haifi mutum amma a lokacin ba su da ciwon suga sai daga baya suka samu, ko dansu na cikin hadarin kamuwa ke nan?
Daga A.A. Nasir
Amsa: Yawanci ciwon suga da ya fara a manyantaka nau’i na biyu ne. Shi kuma nau’i na biyu duk da cewa ana iya gadonsa, halayya ta fi tasiri a kansa ya fi tasiri a nau’i. dabi’ar ciye-ciyen abinci da yanayin jikin mutum sun fi tasiri fiye da gado a wajen samun ciwon suga nau’i na biyu, wanda jama’a da dama suka fi kamuwa. Don haka idan iyayenka na da nau’i na biyu, ba a sa ran za ka kamu, sai dai idan dabi’ar ciye-ciyenka ce za ta sa ka kamu.

Tabbas sha-zumamu na bin fitsarina a wasu lokutan. Yanzu na gane dalili. Ya kamata ke nan na je a gwada ni?
Daga Maman Ishak
Amsa: A’a, ba wai sai fitsari fa mai suga sha-zumamu kan hau ba. Amma dai idan aka cika ganin haka, alama ce ta cewa dole a yi gwaji. Yauwa, don kada a gwada a ga ba ki da matsalar ki ce ko ba daidai aka yi awon ba. Ana iya samun masu lafiya sha-zumamu na bin fitsarinsu. Amma ni dai idan na ga sha-zumamu na kewaye fitsarina to ba makawa sai na je an auna an ga ko lafiya.

Wani lokaci bakina yakan yi dandanon zaki haka kawai ko ban sha abu mai zaki ba. Wannan na nufin matsala ke nan?
Daga Muzammil, Bichi
Amsa: A’a, in dai ba alamun ciwon suga, ba ya nufin matsalar ciwon suga. Sai dai idan kana shakka, yana da kyau a je a yi awon ciwon suga.

Ni kuma ina yawan cin kwan salwa. Ko hakan akwai matsala, kuma ko zai iya kariya daga ciwon suga?
Daga Salisu, Gombe
Amsa: kwan tsuntsun salwa shi ma kamar sauran kwai na tsuntsaye yake, ba ya kawo illa sai idan ana cinsa fiye da kima. An tabbatar dai ya fi kwan kaji sinadarai masu gina jiki na protein da na bitaman, amma ban ga wurin da bincike ya tabbatar cewa a kimiyyance zai iya kariya daga ciwon suga ba.

Ni zafin fitsari ne ke damu na hade da yawan yinsa. Domin idan na tashi da safe nakan yi kamar sau ashirin.
Daga Nasir Y. Sokoto
Amsa: Haba Malam Nasir kada ka ba Sakkwatawa kunya mana. Kana fitsari kusan sau ashirin da safe idan ka tashi hade da jin zogi amma ka zura wa sarautar Allah ido? Ai ko danka ka ga yana haka da gudu za ka nemi a duba lafiyarsa.
Wadannan alamu ba a ce kai tsaye irin na ciwon suga ba ne, sun fi kama da shigar kwayoyin cuta a mafitsara. Amma dai aune-aunen fitsari da jini kam ya same ka.

Ni ina da jiki. Nakan yawan shan lemon maltina, kwalba biyu a rana. Ya zan yi na rage jikin? Kuma shin tunani ne ke jawo hawan jini ko me?
Daga Yusuf Muhammad
Amsa: An ba da bayanai na hanyoyin rage ciye-ciye da rage kiba a makon da ya wuce. Hawan jini kamar ciwon suga, a mafi yawan lokuta gado da kiba su suka fi kawo shi, fiye da damuwa da tunane-tunane.

Idan na ci abincin dare na kwanta sai na wayi gari da ciwon ciki. Ko me ya sa?
Daga M. M. Kaduna
Amsa: Za ta iya yiwuwa akwai dalilai da dama da kai kadai ka sani, amma dai a likitance akan yi hasashen watakila ko abincin bai narke ba sosai kafin ka kwanta ko kuma ba abin da cikinka ke bukata ba ne a wannan lokaci. dabi’ar a ci a kwanta da wuri, wato ba a ba da tazarar awanni ba tsakani ba ga ciki kadai take illa ba, har ma ga jiki gaba daya, domin za ta iya sa kiba, ko da kuwa kibar boye ce, mutum bai lura yana kiba a fili ba, wadda ita kuma wannan za ta iya jawo matsalar ciwon suga.

Me ke kawo yawan shan ruwa duk bayan mintuna talatin mutum ya sha ruwa leda hudu?
Daga Aliyu Unguwar Tudu
Amsa: E, wannan na daya daga cikin alamun ciwon suga, amma kusan yawan fitsari a ciwon suga shi ne gaba fiye da yawan shan ruwa. Don haka kai ma idan kana yawan fitsarin, dole ka je a yi maka gwaje-gwajen.

Me ke kawo yawan susar jiki, musamman ta wajen ciki?
Daga Shu’aibu Cham
Amsa: Yawanci canjin yanayi ko na abinci ko na ruwa shi ke kawo kaikayin jiki. Amma akwai wani nau’in kaikayin jiki na masu ciwon suga saboda sukarin yana taruwa a karkashin fata. Don haka wanda yake samun irin wannan kuma abu ya-ki-ci-ya-ki-cinyewa sai ya ga likitan fata.

Ni kuma idan na sha ruwa lokacin da nake cin abinci ne nake jin kullewar cikin. Wace hanya ya kamata na bi wajen kaucewa hakan?
Daga Anas, Kurya
Amsa: E, hanyar da za ka bi ka kaucewa hakan ita ce ka rika bari sai ka gama cin abincin da ’yan mintuna da cin abincin sai ka dan sha kadan, can an jima ma haka. Idan hakan bai yi magani ba sai ka dangana da ganin likita ido-da-ido.

Mene ne amfanin agada ga jikinmu, don ni ina cin danya da wadda aka soya sosai.
Daga RBM. Kano
Amsa: Agada ’yar uwar ayaba ce, kusan duk sinadaransu daya (sinadaran bitaman na rukunin A da C, da ma’adinin potassium) sai dai idan ba a dafa ko soya, ko gasa ta ba, tana da tauri, ba kamar ayaba wadda akan ci danya ba. Wasu masana ilmin cimaka suna ganin yawan cin ta idan ba ta ji wuta ba zai iya kawo kullewar ciki.

Shin da gaske ne yawan cin naman shanu na iya janyo ciwon daji?
Daga Haiman Ra’ees, Kaduna
Amsa: kwarai haka ne, yana iya kawo ciwon daji na babban hanji. Ai a shekarar da ta wuce mun dauki wannan bayani sukutum mun tattauna shi, a lokacin da Hukumar Lafiya ta Duniya ta fitar da sanarwar cewa tabbas masu cin jan nama a kullum (ba jefi-jefi ba) suna cikin hadarin kamuwa da ciwon daji na hanji

Mai ciwon tarin fuka idan ya sha magani ya warke, ko zai iya aikin soja?
Daga Abdullahi Damagari
Amsa: kwarai kuwa, in dai an tabbatar masa a asibiti ba sauran kwayar cutar a huhunsa, kuma shi ma ya ji zanzan na tsawon lokaci ba tari ba rama, ba wani laulayi da rashin kuzari, tabbas zai iya neman shiga aikin soja.

Wai da gaske ne akwai jinin da kwayar cutar HIb ba ta kamawa? Ni na san wadanda suke da iyali mai ciwon amma su ba su da shi.
Daga Abdullahi Amaco
Amsa: E, da gaske ne akwai wadanda kwayar cutar ba ta yi wa komai. Amma dai idan ba su yi gwaji ba, yana da kyau su je a auna.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited