Amsoshin Tambayoyi 25
Tuesday 27 June 2017     2 Shawwal 1438

Aminiya

A+ A A-

Amsoshin Tambayoyi 25

Shin idan mace mai ajin jini ‘O’ ta auri wani shi ma mai ajin jini ‘O’ ko akwai abin da zai iya samun ’ya’yansu?

Daga Zuwaira Sokoto

Amsa: Ya danganta da ko ajin jinin (+) ne, ko (-). Idan dukansu ‘O+’ ne ba damuwa, idan dukansu ‘O-‘ ne, shi ma ba damuwa. Amma idan daya cikinsu ‘O+’ ne, dayan kuma ‘O-‘ akwai damuwa. Kai ba a ajin ‘O’ kadai ba, ko a wane aji ne aka samu (+) da (-) a tsakanin ma’aurata akwai matsala. Kuma yawanci matsalar ba ta nunawa a yaron farko, sai a mabiyansa wadanda kusan mutuwa suke a ciki. Amma idan ana awo a asibiti za su gano hakan, kuma su kiyaye aukuwar matsalar.
Wane ajin jini ne ba ya kamuwa da kwayar cutar kanjamau?
Daga Mahmood Okene
Amsa: Kowane irin ajin jini zai iya kamuwa da kwayar cutar kanjamau. Ida nana maganar wadanda ba sa kamuwa da ciwon kanjamau, ba maganar ajin jini a ciki, abin da kan sa su jininsu ba ya kamuwa a jikin fararen kwayoyin halittun jini suke, su kuma sinadaran bambance ajin jini a jikin jajayen kwayoyin halittun jini suke.
Ni shekaruna 33, yarana 8, kuma a yanzu haka ina da wani juna biyun. Amma sai na rika ganin jini jefi-jefi. Ko hakan na nufin mahaifata ta fara gajiyawa ko bari?
Daga Maman Yara
Amsa: A’a, yawanci ganin jini jefi-jefi a juna biyu daga shi kansa cikin ne ba mahaifa ba, kuma zai iya zama alamun farko na bari. Koma dai mene ne a wurin awo ne za a tantace dalilin. Mu dai kawai watakila shawarar da za a kara miki da ita ta bangaren lafiyar mahaifar taki ba ta wuce ki nuna wa maigidan shawarar likita ta sama miki dabarar hutun haihuwa, ko da ta shekaru biyar ne, don jikinki da mahaifar su huta, yaranki su yi wayo, kafin ki ci gaba, ganin cewa har yanzu kina da karancin shekaru.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited