Amsoshin tambayoyi daban-daban 1
Saturday 24 June 2017     29 Ramadan 1438

Aminiya

A+ A A-

Amsoshin tambayoyi daban-daban 1

Mece ce illar taba ruwan batir. Me ya sa idan mutum ya taba batir da ya fara ruwa sai ya ji wani irin dandano a bakinsa?

Amsa: Akwai guba a tattare da ruwan batir. Wannan gubar kuwa a kimiyance ita ce ta sinadarin lead, wato dalma, wanda shi ba ya illa lokaci guda, sai dai ya taru a sassan jiki ya rika illa a hankali a hankali. Wato idan aka taba shi da hannu, yana bin fata ya bi jini, a je a ajiye a sassan jiki irinsu hanta, koda, kwakwalwa dasashi (abin da ya sa ke nan ake jin dandonsa a baki), da sauransu. A hankali kuma jiki zai nemi fitar da shi ta bayan gida da mafitsara, amma idan yawan gubar ya kai ya kawo, ko dai idan ana tabawa a kullum (kamar a masu aikin hakar ma’adinai ko masu caza batira) kafin jiki ya fitar din ya riga ya yi illa. Don haka ne masu aiki a irin wadannan wurare akan bukaci su samu kayan kariya daga tabawa ko shakar wannan gubar.

Don haka idan sau daya aka taba, kuma kadan ne, da an wanke wurin shi ke nan, amma a masu mu’amala da shi, masu tabawa, kullum ba kayan kariya, suna cikin hadari babba, na mutuwa da ciwon sassan jiki kamar hanta da koda. Yara kuma abin ma saurin kashe su yake yi. Ai idan kin tuna a shekarun da suka wuce gubar ta yi sanadiyyar rasa daruruwan yara wadanda ke bin iyayensu aikin hakar dalmar, a jihohin Zamfara da Neja.
Ko shafa hodar aski a maza yana da wata illa? Kuma mene ne a ciki na sinadaran hodar aski?
Daga Adamu Gwaram, Jigawa
Amsa: A iya bincikena a likitance, ba a fitar da labari ko rahoto ko mukala a kan wata illa da akan samu idan an shafa hodar aski, ko da na tsawon lokaci, kamar yadda aka bayar a kan ruwan batir ba, in ban da kuna. Wato da yake hodar tana da karfi, ba ko wace irin fata ce ke iya daukar zafinta ba. Domin wasu idan suka shafa dan wannan zafin da suke ji, da sun wanke wurin suke ganin wurin ya yi dau, kamar kuna, kuma sai ya yi kwanaki bai warke ba. Mun san akwai rade-radin cewa zai iya kawo kansa, amma wannan har yanzu ba wanda ya fito karara ya nuna wa masana hakan.
Da gaske ne sinadarin Talc na cikin hodar da muke shafawa tana iya taruwa ta kawo ciwon kansa?
Daga Maman Shahida
Amsa: To, shi ma wannan bincike ya nuna ba haka ba ne. A shekarun baya kafin shekarun 1970 ana cikin amfani da wannan sinadari na Talc a hoda, sai aka gano yana kunshe da sinadari na asbestos mai kawo kansar huhu idan ana yawan shakarsa. Amma tun da aka gano haka, sai aka fara tsabtace shi sinadarin Talc din, ya zama ba wancan sinadarin mai asbestos.
Duk da haka dai, wasu masana sun zo sun fara bincike a kan ko shi wannan sinadari idan ana yawan shafa shi a jiki, musamman a mata, ko yana iya kawo ciwon kansa na ’ya’yan kwan mace, wato obary, amma dai har yanzu ba wanda zai ce kai tsaye akwai alakar.
Nakan yi tafiya ta tsawon awanni uku, ko ma fiye. Shin hakan zai iya yin illa ga lafiyata?
Daga Haiman Ra’es, Kaduna
Amsa: kwarai kuwa, Malam Ra’es, ai ka zurfafa. Kuma zurfafawa a kowane irin abu ba shi da dadi, kuma ba shi da amfani, domin a likitance mu dai ba wanda mukan dorawa wani tafiyar kafa ta tsawon awanni, domin ko jinyar ciwon kafar da zai biyo bayan irin wannan tafiyar ai wahala ce.
Ni kuma idan ina tafiya ina jin kirjina yana daurewa kamar an sa mini barkono. Ko me ke haddasa haka?
Daga Alhaji Musa Jigawa
Amsa: Yana da kyau ka samu ka je a binciki lafiyar zuciyarka, musamman ma idan ka riga ka manyanta, domin za ta iya zama zuciya, wadda ita ciwonta shi ne abin tsoro, ko gymbo a tumbin ciki, ko ma wani abin daban a huhun.
Likita a rubutunka na makon da ya wuce ka rubuta cewa doya da dankali da wake a ajin legumes suke. Wake ne da peas, wato koren wake da danginsu a ajin legumes. Doya da dankali a ajin root and tubers suke.
Daga Bala M.R Kano, Tsohon malamin aikin gona
Amsa: To, babana godiya nake da gyaran. Da fatan masu karatu sun lura.
Akwai wata matsala ne shan shayi da lemon tsami?
Daga Maryam Farin Ruwa
Amsa: A’a, ba wata matsala, za ki iya shan abinki
Ina yawan cin latasa da kabeji da gurji a duk safiya, kafin karin kumallo. Shin hakan akwai matsala?
Daga M.M
Amsa: A’a, ba matsala, in dai ana wanke su sosai kafin a ci, kuma ba sa bata maka ciki, ka ci kayanka. Dama ana so a rika cin kayan ganye da na ’ya’yan itatuwa a kullum. Watakila sai dai ka kara da na itatuwan ke nan, su kuma kamar can da yamma haka.
Ni ina da ciwon gyambon ciki, don haka ne ma nake cin abinci sau hudu a rana. Ko hakan zai iya jefa ni cikin hadarin ciwon suga?
Daga Zainab Gusau
Amsa: E, likitoci da dama suna ganin cin abinci a kai-a kai zai iya rage zafin gyambon ciki, ko ma ya kiyaye aukuwarsa. A hannu daya kuma idan mutum ya cika ciye-ciye da yawa zai iya yin kiba, ya shiga hadarin kamuwa da ciwon suga. To yaya ke nan? To idan irin haka ta faru lissafi ake a sassaita yawan abincin da ake ci, kamar yadda muka taba bayani a baya, kusan kowane kofi ko gwangwani na hatsi da sauran abinci yana da nauyinsa a ma’aunin calories.
Yadda ake shi ne sai a tara abincin ranar mutum na lokaci uku (safe, rana, dare) a raba shi gida hudu. Abin da kamar wuya amma da sauki. Yadda abin yake shi ne; idan mai cin abinci sau uku a rana yana cin rabin biredi da safe, to a yanzu in zai ci abinci sau hudu a rana sai ya rage ya dawo sulusi, wato daya bisa uku. Da hantsi a iya cin dumame, ko abin da ya sauwaka. Da rana idan ya saba cin gwangwanin shinkafa biyu sai ya ci daya, ya hada da ganyaye da ’ya’yan itatuwa. Da yamma ya dan nemi wani abu maras nauyi na shashe baki. Da dare ma a rage girman malmala. A haka mutum zai ci abinci sau hudu ko fiye a rana ba tare da hakan ya taba lafiyarsa ba.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited