Ya ake gane mace ba za ta iya haihuwa da kanta ba?
Saturday 24 June 2017     29 Ramadan 1438

Aminiya

A+ A A-

Ya ake gane mace ba za ta iya haihuwa da kanta ba?

Likita ya za a gane macen da ba za ta iya haihuwa da kanta ba, a ce sai an mata tiyata? Me ya sa kuma yawanci sai an barta ta galabaita kafin a yi tiyatar?

Amsa: Akwai hanyoyi da dama da likitoci, da ma kwararrun ungozomomi kan bi, wajen gane ko mace za ta iya haihuwa da kanta ko ba za ta iya haihuwa da kanta ba. Misalansu su ne; shekarun yarinyar, da tsayinta, da girman jikinta, da girman kugunta, da girman abin da ta ke dauke da shi a ciki (wanda ya ta’allaka ma a kan girman jikin mahaifin), da karfin lafiyarta da sauransu. Wadannan matsaloli wasunsu tun farkon daukar cikin ake ganowa, inda tun a wurin awo za a fada mata sai ta shirya tiyata, wasunsu kuma, musamman a marasa zuwa awo, ba a ganowa sai abu ya zo dab, lokacin haihuwa ya yi. Wannan tiyata wadda ake yi dab da haihuwa, wato na kar-ta-kwana, ko Emergency, wanda dalilinta ke zuwa ba tsammani, a kusan kowane sashi na duniya, shi ne ya fi yawa, ballantana a irin kasashenmu, inda wasu ba su dauki awo da muhimmanci sosai ba, inda masana suka ce shi ne fiye da kashi 70 cikin 100.

Wato abin dai nufi a nan shi ne kusan tiyatar haihuwa da ake a irin kasashenmu ta kar-ta-kwana ta fi ta wadda aka sa wa rana. Shi ya sa za a ga kamar an bar mace tana nakuda cikin wahala, daga baya kuma a ce sai an yi tiyata. Su wadanda aka sa wa ranar a wurin awo wadanda aka duba su aka tantance wadancan abubuwa na lafiyar uwa, da wuya su sha irin wannan wahalar.

Muna da yaro dan shekara biyu da kusan rabi, wanda ke fama da matsalar cin kasa. Mun yi iya yinmu domin ya bari, amma abu ya gagara. Shi ne muke tambaya ko akwai magani?
Daga Ahmad I., Kabo da Maman Mama
Amsa: To ko dai Mallaman bakin wannan shafin ne? Domin a wannan kafa an sha zayyana cewa cin kasa a yara (da ma a wasu mata, musamman masu juna biyu) alamu ne na rashin isasshen jini a jiki. Wato kusan zai wuya a ce wannan yaro, da ma sauran yara masu cin kasa, jinin jikinsu isasshe ne. Don haka in dai yana cin abinci sosai, abinci mai kara jini kawai za ku rika nema masa kamar hanta, nama, ganyen alayyahu, da wake (kamar faten wake mai alayyahu ke nan), ko wasu abincin gwangwani na kantina din nan. A kalla idan aka ce ya samu daya daga cikin wadannan a kullum, cikin ‘yan satuttuka za ku sha mamaki. Amma idan abin ya ki dorewa kuma za a iya komawa gidan jiya.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited